Gwamnatin Tinubu Ta Dakatar da Muhimmin Aikin da Buhari Ya Fara a Najeriya
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya jaddada cewa gwamnati ta dakatar da aikin jirgin saman Najeriya har sai baba ta gani
- Tun farko dai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da jirgin Nigeria Air kwanaki uku kafin ya sauka daga mulki
- Amma bayan gano wasu kura-kurai, Gwamnatin Bola Tinubu ta dakatar da aikin a watan Agusta, 2023 ta bakin Mista Keyamo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta ƙara jaddada cewa ta dakatar da aikin jirgin saman Najeriya.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai na cikar Bola Tinubu shekara ɗaya a kan mulki a Abuja ranar Litinin.
Buhari ya kaddamar da jirgin Nigeria Air
A 2023, ma’aikatar sufurin jiragen sama a karkashin tsohon minista Hadi Sirika ta kaddamar da kamfanin jirgin saman Najeriya watau 'Nigeria Air'.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Cable ta ruwaito, an kaddamar da jirgin sama na farko kwanaki uku kafin karshen gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.
Lamarin dai ya ta da ƙura a fadin Najeriya musamman kan tsarin yarjejeniyar mallaka, wanda ya ba kamfanin jiragen saman ƙasar Habasha kashi 49%.
A watan Agusta 2023, Keyamo ya ba da sanarwar cewa an dakatar da aikin jirgin saman Najeriya wanda Buhari ya fara gab da zai bar mulki, The Nation ta ruwaito.
Gwamnatin Tinubu ta jaddada dakatarwar
Da yake ƙarin bayani a taron manema labarai na ministoci da aka yi a Abuja don murnar cikar Tinubu shekara daya a kan mulki, Keyamo ya ce matakin dakatar da aikin na nan har yanzu.
"Mun dakatar da aikin har kawo yanzu saboda maganar gaskiya ba jirgin saman Najeriya ba ne, kawai fentin Najeriya aka yi wa jirgin amma kamfanin jirgin ƙasar Habasha ne ke kokarin amfani da tutar mu.
"Dole kamfanin Air Nigeria ya zama na ‘yan kasa, dole ne ya zama Najeriya ce ta mallake shi, kuma ya zama wanda zai kawo ci gaban Najeriya, ba wai a tura kashi 50% na ribar ga wata kasa ba."
- Festus Keyamo.
Hadimin Ganduje ya caccaki Abba
A wani rahoton na daban, an ji hadimin shugaban APC na ƙasa ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yunƙurin wargaza ayyukan da Abdullahi Ganduje ya yi.
Cif Oliver Okpala ya ce abubuwan da ke faruwa a Kano wata manaƙisa ce da aka shirya da nufin ganin bayan tsohon gwamna Ganduje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng