Kwana 2 da Karbar Mulki, Sarki Sanusi II Ya Nada Sabuwar ‘Jakadiyar Sarkin Kano’
- Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nada Hajiya A’in Jafaru Fagge a matsayin Jakadiyar Sarkin Kano
- Wannan nadin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Muhammadu Sanusi II ya koma kan karagar sarautar Kano
- A hannu daya, zanga-zanga ta barke a wasu sassa na jihar Kano inda ake kira ga gwamnati da ta tsige Sarki Sanusi II
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Kwanaki biyu da hawa kan kujerar mulki, sabon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya fara yin sauye-sauye ga hadiman cikin fada.
An nada Jakadiyar Sarkin Kano
A yau Lahadi, muka samu rahoton cewa mai martaba Sanusi II, ya nada Hajiya A’in Jafaru Fagge a matsayin Jakadiyar Sarkin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai tallafawa gwamnan jihar Kano ta fuskar kafofin sada zumunta, Abdullahi I. Ibrahim ya tabbatar da hakan a shafinsa na X.
Abdullahi I. Ibrahim ya wallafa cewa:
"Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya nada Hajiya A’in Jafaru Fagge a matsayin Jakadiyar Sarkin Kano."
Kalli sanarwar a nan kasa:
Jakadiyar Sarkin Kano: Mutane sun magantu
Mutane sun yi martani kan wannan nadi na jakadiya.
@Usman_Tokari:
"Babu 'capacity' yar siyasa a fada"
@shamsumailowco1:
"Hajiya muna taya murna"
@nazeef___:
"Ba lokaci, Allah kawo namu nadin"
@isah_muaaz:
"Yan kwankwasiyya kuna sharafi wallahi, gwamnati ta ku, masarauta ta ku."
@ibrahimchicago:
"Agaishe ki jakadiya"
Zanga-zanga ta barke a sassan Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa zanga-zangar nuna adawa da mayar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II kan kujerar mulki ta mamaye sassan jihar Kano.
A Gaya da Nasarawa inda aka gudanar da zanga-zangar, al’ummar garin sun yi tururuwa a kan tituna domin nuna adawa da dawo da Sanusi II gidan sarautar Kano.
Masu zanga-zangar dai sun zargi gwamnatin jihar da yin amfani da wata manufa ta siyasa wajen rusa sarakunan biyar tare da neman a maido da masarautun nasu da kuma sarkin da aka tsige.
Asali: Legit.ng