Masallaci Ya Rufto Kan Masallata a Legas, An Rasa Rayuka Masu Yawa

Masallaci Ya Rufto Kan Masallata a Legas, An Rasa Rayuka Masu Yawa

  • An shiga jimami a jihar Legas bayan ginin wani masallaci ya rufto kan masallata suna tsaka da gudanar da Sallar Azahar
  • Lamarin wanda ya auku a yankin Papa Ajao na jihar Legas ya yi sandiyyar rasuwar mutane masu yawa waɗanda ba a san adadinsu ba
  • Mutane da dama sun samu raunuka sakamakon ruftowar ginin masallacin yayin da wasu da dama da ba a tantance adadinsu ba suka maƙale a cikin ɓaraguzai

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Ana fargabar mutane da dama sun rasu bayan wani masallaci ya rufto kan masallata a Legas ranar Lahadi da rana.

Lamarin ruftowar masallacin dai ya auku ne a yankin Papa Ajao a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun hallaka dalibai 2 da suka sace a Jami'a, ƴan sanda sun magantu

Masallaci ya rufto a Legas
Masallaci ya rufto kan masallata a Legas Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa masallacin ya rufto ne a lokacin Sallar Azahar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ciro gawarwaki da mutanen da suka samu raunuka da dama yayin da har yanzu ake fargabar cewa akwai sauran wasu da suka maƙale.

Hukumomin ba da agajin gaggawa da masu aikin ceto na ci gaba da ƙoƙarin ganin sun ceto mutanen da suka maƙale a cikin ɓaraguzan ginin masallacin da ya rufta.

Jaridar Nigerian Tribune ta rahoto cewa ba a san adadin yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba sakamakon ruftowar masallacin.

Hakazalika ba a tantance adadin yawan mutanen da suka maƙale ba a.cikin ɓaraguzan ginin yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ganin an ceto au.

Gini ya rufto a Kano

A baya Legit Hausa ta kawo rahoto cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce har yanzu ma'aikata na aikin zakulo waɗanda gini ya rufta musu a Kano.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, SFS Saminu Yusuf Abdullahi ya tabbatar da cewa ana ta aikin ceton rai, kuma babu tabbacin adadin waɗanda su ka rasu.

Gini ya rufto kan jariri

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mazauna jihar Ondo sun shiga tashin hankali bayan gini ya fado kan wata uwa da jaririnta.

Ɗan uwan jaririn da kakarsa sun samu su sha da ƙyar yayin da ake ci gaɓa da jimamin rashin da aka yi na mutum biyun waɗanda suka rasa rayukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel