Hantar Wasu Ta Kada Bayan Tinubu Ya Bayyana Ministocin da Zai Kora Daga Gwamnatinsa

Hantar Wasu Ta Kada Bayan Tinubu Ya Bayyana Ministocin da Zai Kora Daga Gwamnatinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kusa cika shekara ɗaya a kan kujerar mulkin Najeriya bayan ya gaji Muhammadu Buhari
  • Shugaba Tinubu ya shirya sallamar wasu daga cikin ministocinsa waɗanda suka gaza yin abin kirki tun bayan shigarsu ofis
  • Mai shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga shi ne ya bayyana hakan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya korar ministocinsa waɗanda ba su taɓuka abin arziƙi ba.

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa ministocin da suka gaza yin abin da aka sanya su, za su rasa muƙamansu.

Tinubu ya shirya korar wasu ministoci
Tinubu zai kori ministocin da ba su yi abin arziki ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayo Onanuga ya bayyana cewa duk da shugaban ƙasan bai gama yanke shawara ba kan ayyukan da ministocin suka yi, ya umarce su da su aiki wajen cimma abubuwa takwas da gwamnatinsa ta sanya a gaba.

Waɗanne ministoci Tinubu zai kora?

Ya ƙara da cewa waɗanda aka samu da gazawa wajen yin hakan, za a sallame su daga majalisar ministocin shugaban ƙasan.

Shugaban ƙasa Tinubu ya gayawa ministocin cewa zai kore su idan suka kasa taɓuka abin kirki. Ya gaya musu a wajen taron bita shekarar da ta gabata cewa gwamnati na da ajanda takwas, kuma yana son a cimma su."
"Duk waɗanda aka samu da gazawa wajen cimma hakan, za su rasa muƙamansu. Amma har ya zuwa yau shugaban ƙasa bai yanke wani hukunci ba kan hakan.
"Shugaban ƙasa bai ce zai yi wa majalisar ministocinsa garambawul ba. Duk cikin ministocin babu wanda ya yi shekara ɗaya a ofis. Sun fara aiki ne a watan Agusta. Shugaban ƙasa yana so ne su iya kare aikin da aka ba su."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya bayyana wani muhimmin tagomashi da gwamnatinsa ta samu

- Bayo Onanuga

Jigo a APC ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC a na ƙasa a yankin Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya caccaki shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Salihu Lukman ya ce alamu sun ƙara tabbata cewa Tinubu ba zai iya gyara Najeriya ba kamar yadda ya yi a Lagos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng