Sanusi II Vs Aminu Ado: Atiku Ya Yi Magana Kan Rikicin Sarautar Kano, Ya Fadi Mai Laifi
- Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya mayar da martani kan rikicin sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero a Kano
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar PDP ya yi Allah wadai da matakin tura sojoji, inda ya ce hakan zai dagula zaman lafiya da tsaro a jihar
- A cewar Atiku, akwai buƙatar a tunawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu cewa Kano ta yi fice wajen zaman lafiya da tsaro, kuma duk wani yunƙurin tayar da zaune tsaye ba zai yi nasara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da matakin tura sojoji a rikicin sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya ce ba daidai ba ne a ce gwamnatin tarayya ƙarkashin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta yi amfani da sojoji, inda ya ce matakin na da nufin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a jihar.
A cewar Atiku, mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano da kuma sauke Aminu Ado Bayero ya bi tsarin doka kamar yadda aka tanada a kundin tsarin mulki na shekarar 1999.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da sanyin safiyar ranar Asabar 25 ga watan Mayu ne tsohon sarkin Kano, Amin Ado Bayero ya koma jihar bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga sarauta.
Hakan ya sanya gwamnan ya ba da umarni a cafke tsohon Sarkin na Kano wanda sojoji ke ba kariya a gidan sarki da ke Nasarawa.
Sai dai, hukumomin tsaro a jihar sun ce za su bi umarnin kotu ne kawai da ya hana gwamnan mayar da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.
Me Atiku ya ce kan rikicin sarautar Kano?
Yayin da Atiku ya yi shiru game da hukuncin da kotun ta yanke, ya lura cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Tinubu ta tuna cewa Kano an santa da zaman lafiya.
A wani rubutun a shafinsa na X, Atiku ya bayyana cewa:
"Muna bukatar mu tunatar da gwamnatin Tinubu cewa jihar Kano ta shahara da zaman lafiya da kwanciyar hankali wanda ya kwashe dubunnan shekaru sannan duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaman lafiyan Kano za a yi masa turjiya."
"A baya lokacin da aka tuɓe Muhammadu Sanusi II a ranar 9 ga watan Maris 2020, an ci gaba samun zaman lafiya a Kano ba tare da wani hargitsi ba."
Sanusi II ya gana da shugabannin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya gana da shugabannin tsaro a jihar tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar Sarkin Kano.
Ganawar Sarkin da shugabannin tsaron na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zama cikin halin rashin tabbas kan rikicin sarautar Kano.
Asali: Legit.ng