Sarkin Kano: Lauya ya Lalubo Lungun da Abba Ya Saba Doka Wajen Maido Sanusi II
- Abba Hikima yana ganin gwamnatin Kano ba ta da madogara ta fuskar shari’a wajen dawo da Muhammadu Sanusi II
- Lauyan ya ce dokar da Abba Kabir Yusuf ya fake da ita wajen nada sabon Sarki ta daina aiki lokacin Abdullahi Ganduje
- Hikima ya bayyana cewa tun da an soke dokar a 2019, babu ta yadda za a maido Sanusi II kan mulki ta irin wannan salo
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Abba Hikima lauya ne wanda ya shahara musamman a garin Kano, ya yi magana game da rikicin masarauta da ake yi.
Masanin shari’ar ya na da ra’ayin gwamnatin Abba Kabir Yusuf da majalisar dokoki sun yi kuskure wajen nada sabon sarkin Kano.
Abba Hikima ya ga kuskuren maido Sanusi II
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, Abba Hikima ya yi ikirarin cewa ba a bi doka yadda ya kamata ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya ce tun farko bai damu da sha’anin masarauta ba, a nasa ganin ma ana zuzuta sarakuna da matsayinsu a cikin al’umma.
Amma a matsayinsa na lauya, ya ga bukatar ya tofa albakarcin bakinsa musamman a inda yake ganin an tafka ba daidai ba a Kano.
Sanusi II: 'Kuskuren' da Gwamna Abba ya yi
Hikima ya ce da safiyar Juma’a ya ji Abba Kabir Yusuf yana kafa hujja da dokar sarakuna ta 1984 wajen maido Muhammadu Sanusi II.
Ganin yadda gwamna ya dogara da wannan doga ya sa lauyan ya shiga lalube, kuma ya gano cewa ta daina aiki tun a shekarar 2019.
A cewar Hikima, sashe na 51 na dokar masarautar Kano ta shekarar 2019 ta shafe wancan tsohuwar doka da aka kirkiro lokacin sojoji.
Binciken lauyan ya tabbatar masa da haka, ya kuma gano cewa sabuwar dokar masarauta ta 2024 ta rushe wancan doka ta 2019.
An yi nadin Sanusi II kan yashi kenan?
Inda matsalar ta ke, Hikima ya ce gwamnatin Kano ba ta farfado da dokar masarautun 1984 wajen sake nada Sanusi II a jiya ba.
Rusa dokar da aka kirkiro lokacin Abdullahi Ganduje bai nufin dokar 1984 ta dawo rai, wanda da ita Abba ya yi nadin sabon sarkin Kano.
A karshe lauyan ya jefi gwamnatocin Kano da garaje wajen cusa kai a sha’anin masarauta wanda ya jawo sa bakin jami'an tsaro.
An aikawa Sarki Sanusi II sako
An ji labari tsohon ‘dan takaran gwamnan jihar Kano, Muazu Magaji ya fadi abin da ya jawowa Muhammadu Sanusi II matsala a baya.
Magaji ya ce idan Muhammadu Sanusi II Sarauta ya dawo ya yi, to dama ita ta haife su, amma idan siyasa zai yi, za su yake shi a APC.
Asali: Legit.ng