Yadda ’Yan Najeriya Za Su Rika Shiga Tapswap a Saukake, Batun Matsalar Ya Fito
- Wani dan Najeriya ya samar da mafita ga matsalar shiga Tapswap da yawancin 'yan Najeriya ke fuskanta a kwanan nan
- Ya fadi sunan manhajar 'yan Najeriya za su iya saukewa domin shiga Tapswap da kuma tara sulalla 1.5m a take
- A zantawar mu da masanin crypto, Nura Haruna Maikarfe, ya gargadi 'yan Najeriya kan amfani da VPN a wayoyinsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A cikin 'yan kwanakin, yawancin 'yan Najeriya da ke harkar hakar ma'adanan Taspwap sun kasa samun damar shiga manhajar da ke kan Telegram, wanda ya haifar da damuwa.
Idan ba a manta ba, a baya mun ruwaito yadda wata matashiya ta kwantarwa 'yan Najeriya hankali kan wannan matsalar, yayin da TapSwap ya ce yana kan yin gyara.
Wani dan Najeriya Ambrose Nwaogwugwu, ya yi bayanin hanyar magance wannan matsalar a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ake shiga TapSwap a saukake
Ambrose ya ce mutanen da har yanzu ba sa iya shiga Tapswap za su yi amfani da manhajar sadarwa mai zaman kanta (VPN) a yayin da za su shiga Telegram.
Ambrose ya bayyana cewa ya na yin amfani da manhajar X-VPN domin samun damar shiga Tapswap, kuma amfani da X-VPN kyauta ne.
Ya kara da cewa, ta hanyar amfani da wannan manhajar ta VPN, ya samu damar tara tsabar sulallan Tapswap miliyan 1.5.
Yadda ake tara sulallan Tapswap 1.5m
1. Da farko, za ka fara bude manhajar VPN din, ka ba ta izini ta aika sadarwa ga wayarka.
2. Daga nan sai ka garzaya zuwa Telegram domin yin rijista da Tapswap a nan likau din.
3. Bayan Tapswap din ya bude, ka bude inda aka rubuta 'Tasks'.
4. Idan ka kammala wadannan aikatau din da aka sa ka, sai ka koma kan VPN din ka canja adireshin kasa zuwa Burtaniya, Jamus da Amurka.
5. Kowace kasa idan ka zaba, za ka koma Tapswap ka yi aikatau din da aka ba ka, a haka za ka tara sama da sulalla miliyan 1.5 a dan kankanin lokaci.
"Amfani da VPN na da hatsari" - Nura Maikarfe
Sai dai a zantawarmu da masanin crypto, Nura Haruna Maikarfe, ya gargadi 'yan Najeriya kan amfani da VPN a wayoyinsu domin yana da hatsari.
Nura Maikarfe ya fara da cewa mutane suna amfani da VPN domin dalilai daban-daban, wasu saboda ba sa san a ga bayanin daga inda suke hawa intanet, ko domin tsaro, wasu kuma saboda suna son canja kasar da suke.
Masanin ya ce matsalar farko ta VPN shi ne yana raunana tsaron wayar mutum ta yadda masu kutse za su iya shiga ko ina a wayar su saci bayanai ko kudin mutum a banki.
Na biyu kamfanonin VPN na iya sayar da bayanan sirrin mutum ga wasu mutane daban, misali, bayanan shiga shafuka ko manhajar banki ko asusun shafukan sada zumunta.
Haka zalika, Nura Maikarfe ya yi zargin cewa matsalar da TapSwap ta samu ba zai rasa nasaba da yawan amfani da VPN da aka yi domin tara sulalla masu yawa ba.
Matashi ya 'samu' N9m a Notcoin
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani matashi ya yi ikirarin cewa ya samu Naira miliyan 9 bayan ya sayar da Notcoin din da ya tara.
Matashin ya bayyana hakan ne ga mabiyansa yayin da ya ke nuna murna da irin makudan kudin da ya samu daga hakar ma'adan crypto (ba mu tabbatar da ikirarin ba).
Asali: Legit.ng