"Wannan ba Cigaba Ba ne': Hadimin Buhari Ya Caccaki Majalisa Kan Rusa Masarautun Kano
- A yau ne majalisar dokokin Kano ta rusa masarautun jihar guda biyar tare da shirin dawo da sarki Muhammadu Sanusi II
- Kudirin da majalisar ta tabbatar ya cigaba da tayar da kura daga cikin da wajen jihar ta yadda al'umma ke bayyana ra'ayoyi mabanbanta
- Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya tofa albarkacin bakinsa kan rusa masarautun na Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rusa masarautun jihar Kano da dawo da shirin Muhammadu Sanusi II ya cigaba da jan hankulan al'umma a ciki da wajen Najeriya.
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bayyana ra'ayinsa kan lamarin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Bashir Ahmed ya soki abin da majalisar ta yi tare da cewa hakan ba zai kawo cigaba ga jihar Kano ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bashir Ahmad yana son yawan masarautu
A cikin sakon da ya wallafa, Bashir Ahmad ya ce yawan masarautun zai kara kawo cigaba a cikin al'umma musamman a wannan zamanin da muke ciki.
Ya ce mafi amfanin masarautu a yau shi ne kusantar al'umma ta yadda za su rika jin kukansu, saboda haka yawansu zai kara kusantar da su ga al'umma.
Masarauta 1 ba ta dace da Kano ba
Har ila yau Bashir Ahmad ya koka kan mayar da Kano karkashin masarauta daya duk da dimbin al'umma da Allah ya yi ga jihar.
Ya ce abin takaici ne a ce ana samun kananan jihohi da masarautu sama da 10 amma a ce Kano na da masarauta guda daya kacal.
Meya kamata majalisar Kano ta yi?
Bashir Ahmad ya ce da majalisar dokokin na son cigaban jihar Kano, za ta yi kokarin kirkiro sababbin masarautu ne a kan guda biyar da ake da su a jihar.
Idan aka samar da karin masarautun, a cewarsa gwamnan jihar zai fi jin dadin tafiyar da mulki cikin sauki.
DSS sun mamaye fadar Kano
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da rahoton rushe masaurautun Kano ya bazu, jami'an DSS sun mamaye fadar mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.
Jami'an tsaron sun tare kofar shiga fadar sarkin da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar yau Alhamis, 23 ga watan Mayu domin tabbatar da tsaro.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng