Majalisa Ta Tsige Sarkin Kano Aminu Ado Bayero? Shugaban Masu Rinjaye Ya Yi Bayani

Majalisa Ta Tsige Sarkin Kano Aminu Ado Bayero? Shugaban Masu Rinjaye Ya Yi Bayani

  • Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Kano ya ce kudirin dokar da suka yi ya soke dukkan sarakunan da Ganduje ya naɗa
  • Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na cikin waɗanda wannan matakin ya shafa tare da sauran sarakuna huɗu
  • Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa ya ce a halin yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf kaɗai ke da ikon naɗa sabon sarkin Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano, Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa ya ce a halin yanzu babu sarki ko daya a jihar Kano.

Ɗan majalisar ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan majalisar dokokin ta warware dokar masarautun Kano da tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya kirkiro.

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar DSS sun mamaye fadar mai martaba Sarkin Kano

Kakakin majalisar Kano, Isma'il Falgore.
Shugaban masu rinjaye na majalisar Kano ya sanar da tsige sarakuna 5 Hoto: Isma'il Falgore
Asali: Twitter

Ya ce majalisar ta tsige dukkan sarakuna biyar kuma ta umarci a koma asali na Sarki ɗaya wanda aka gada tun lokacin jihadin Shehu Usman Dan Fodio, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu Bayero na cikin waɗanda aka tsige?

"Kudirin da muka amince da shi ya soke sabbin masarautu guda 5 da aka ƙirƙiro, sannan zamu koma sarki daya tilo a Kano wanda muka gada tun lokacin jihadin Shehu Usman Dan Fodio. 
"Wannan shi ne abin da kudirin ya ƙunsa a halin yanzu amma muna da shiri a ƙasa na ƙirƙiro karin Sarki mai daraja ta biyu bayan wannan. Ma'ana an tsige sarakuna 5, babu wani Sarki a Kano yanzu.
"Wuƙa da nama na hannun mai girma gwamna, a yanzu shi ke da damar naɗa sabon sarki. Kudirin ya kuma ba gwamna damar ya sa masu naɗa sarki su zaɓi wanda ya dace."

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

- Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa.

Gwamna zai sa hannu a dokar masarauta

Shugaban masu rinjayen ya ce a yanzu suna dakon gwamna ya rattaba hannu kan kudirin idan ya so ko ya umarci masu naɗin sarki su zaɓi sabon sarkin Kano.

Ya kuma roƙi ɗaukacin al'ummar jihar Kano su mara masu baya domin wannan ci gaba ne da ke nuna akwai haɗin kai a jihar, The Nation ta ruwaito.

Jami'an DSS sun dira fadar sarkin Kano

A wani rahoton kuma jami'an hukumar tsaron farin kaya watau DSS sun mamaye fadar mai martaba Sarkin Kano , Alhaji Aminu Ado Bayero.

Wannan na zuwa ne yayin rahotanni suka bazu cewa majalisar dokokin jihar ta tsige Sarki Aminu da sauran sarakuna huɗu da tsohon gwamna ya naɗa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel