EFCC: An Bukaci Binciken Abokin Takarar Atiku Abubakar a 2023, Ifeanyi Okowa

EFCC: An Bukaci Binciken Abokin Takarar Atiku Abubakar a 2023, Ifeanyi Okowa

  • Kungiya mai yaki da cin hanci da rashawa ta yi kira kan binciken tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa
  • Kiran ya biyo bayan korafi da kungiyar ta shigarwa hukumar EFCC kan tsohon gwamnan a watannin baya
  • Ifeanyi Okowa dai ya kasance abokin takarar Alhaji Atiku Abubakar a jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar 2023

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - Kungiya mai yaki da cin hanci da rashawa (NACAT) ta bukaci binciken tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

OKOWA IF
Ana neman EFCC ta binciki tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa. Hoto: Dr Ifeanyi Arthur Okowa
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kungiyar ta yi kiran ne ga hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

Shugaban kungiyar, Tega Oghenedoro ya ce abin takaici ne matuka yadda hukumar EFCC ta yi shiru kan tsohon gwamnan duk da cewa an shigar mata da korafi.

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado badakalar N2.17bn a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okowa da EFCC: Jawabin shugaban NACAT

Shugaban kungiyar ya ce mutane da dama da kungiyoyi sun shigar da korafi kan badakalar da ake zargin tsohon gwamnan amma har yanzu hukumar ta kasa tabuka komai. Ga abin da yace:

"Mun rubuta korafi watanni da suka wuce, haka zalika wasu dattawa daga jihar Delta sun shigar da korafi a kan Okowa amma har yanzu babu wani bayani daga EFCC ko ICPC."

-Shugaban kungiyar NACAT, Tega Oghenedoro

Kiran shugaban NACAT ga EFCC

Shugaban NACAT ya yi kira ga EFCC kan cewa ya kamata ta fara binciken Ifeanyi Okowa kamar yadda ta fara binciken tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

A cewarsa EFCC tana kyale tsofaffin gwamnoni da suka aikata laifuffukan cin hanci da rashawa daga Arewa amma suna kyale na kudu, rahoton Peoples Gazette.

EFCC za ta iya cafko mutumin Atiku

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Bola Tinubu ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya," Dattijon Arewa

Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya kasance abokin takarar Atiku Abubakar a karkashin jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar shekarar 2023.

NACAT ta ce idan har hukumar EFCC ba za ta yi halin maza kan kama Ifeanyi Okowa ba to ya kamata ta kyale Yahaya Bello ma kawai.

Haduwar Atiku da Obi ta ja hankalin APC

A wani rahoton, kun ji cewa da alamu hankalin APC ya fara karkata kan yadda dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ke tattaunawa da takwaransa na LP, Peter Obi.

Ana ganin shugabannin biyu na saka labule domin tattaro dabarun kwace mulkin kasar nan daga hannun shugaba Bola Ahmed Tinubu a kakar zaben 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng