Saurautar Kano: Yau Za a Daddale Kan Yiwa Dokar da Ta Tsige Sanusi II Garambawul
- A yau ne majalisar dokokin jihar Kano za ta zauna domin karatu na uku kan dokar da za ta yiwa masarautu sabon garambawul
- Ana sa ran cewa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf zai sa hannu kan sabuwar dokar domin a samu ikon zartar da ita nan-take
- A lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje aka kirkiro dokar da ta raba masarautar jihar zuwa gida biyar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - A yau Alhamis, 23 ga watan Mayu ne ake sa ran majalisar dokokin Kano za ta yi karatu na uku kan kudirin gyaran dokar masarautun jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da zarar majalisar ta zartar da gyaran, gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf za iya saka hannu kan sabuwar dokar a koda yaushe.
Abin da ya faru jiya a majalisar Kano
A jiya Laraba dai an hango jami'an tsaro sun mamaye majalisar a lokacin da za a yi karatu na biyu kan kudirin gyaran dokar masarautun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan majalisun jihar daga ɓangaren jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar da jami'yyar adawa ta APC duk sun halarci zaman majalisar domin karanta kudirin dokar.
Wanda ya kawo kudurin gyara masarautun
An dade ana rade-radin cewa sabon gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf zai bukaci gyara dokar idan ya samu nasara kuma bayan nasararsa an zuba ido domin ganin ta ina lamarin za fara.
Ana haka ne sai dan majalisa mai wakiltar Dala kuma shugaban masu rinjaye a majalisar, Lawal Hussaini ya bijiro da kudirin gyaran.
Yaushe aka kirkiro dokar da za a gyara?
A shekarar 2019 ne karkashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje aka kirkiro dokar da ta samar da masarautu biyar a jihar.
Masarautun da dokar ta samar a wancan lokacin su ne Kano, Bichi Rano, Gaya da Karaye. Amma dokar ta bayyana cewa masarautar Kano ita ce jagora.
Iliyasu Kwankwaso ya ajiye sarauta a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dokoin jihar Kano ta amince da kawo gyara kan dokar da ta jawo raba kan masarautar jihar a shekarun baya.
Biyo bayan lamarin, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ajiye sarautar sarkin yakin masarautar Karaye saboda nuna adawa da gyaran da majalisar za ta yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng