Gobara Ta Tashi a Sakatariyar Gwamnatin Jihar Kaduna, Ta Yi Barna
- Gobara ta tashi da tsakar rana a sakatariyar gwamnatin jihar Kaduna inda ta laƙume wasu ofisoshi a ranar Laraba, 22 ga watan Mayun 2024
- Gobarar wacce ta lalata wasu daga cikin ofisoshin da ke sakatariyar ta tashi ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana a ranar Laraba
- Wani shaidar ganau ba jiyau ba ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka ba sakamakon tashin gobarar, sai dai lalacewar kayan ofis da wasu sauran kayayyaki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - An samu tashin gobara a sakatariyar gwamnatin jihar Kaduna a ranar Larabar nan.
Gobarar wacce ta tashi a sakatariyar da ke kan titin 'Independence Way', ta lalata wasu ofisoshi da ke wajen.
A cewar wani shaidar ganau ba jiyau ba mai suna Malam Ibrahim Mohammed wanda ma'aikacin gwamnatin jihar ne, gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 2:30 na a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kaduna: Menene ya haddasa gobarar?
Shaidan ya bayyana cewa ba a gano musabbabin tashin gobarar ba amma ana zargin cewa ta tashi ne saboda wutar lantarki, rahoton jaridar Blueprint ya tabbatar.
Malam Ibrahim Mohammed ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, inda ya ƙara da cewa kayan ofis ne da sauran wasu kayayyaki kawai suka ƙone sakamakon gobarar.
Gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan tashin gobarar har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Gobara ta tashi a gidan minista
A baya Legit Hausa ta kawo rahoto cewa an samu tashin babban gobara a gidan karamar ministan babban birnin tarayya (FCT) Abuja, Dakta Mariya Mahmoud.
Gobarar ta fara tashi ne a gidan da ke unguwar Asokoro cikin babban birnin tarayya Abuja da rana tsaka inda ta tafka gagarumar ɓarna.
Gobara ta laƙume gidan Shekarau
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a gidan tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a ranar Lahadi da daddare.
Gobarar wacce ta auku a gidan tsohon sanatan wanda ke Mundubawa, ta lalata ɗakin matarsa ta uku, Halima Shekarau, bayan ta fara daga ɗakin girkin da ke gidan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng