Malamin Addini Ya Boye N1m da Aka Tura Bisa Kuskure Wajen Aiko Sadakar N100,000

Malamin Addini Ya Boye N1m da Aka Tura Bisa Kuskure Wajen Aiko Sadakar N100,000

  • Yan sanda sun kama faston da ake zargi da yin cuwa0cuwar makudan kudi da mai zuwa cocinsa ya tura masa bisa kuskure
  • Duk da cewa faston ya tabbatar da shigar kudin asusun bankinsa, ya bayyana dalilan da suka sa ya ki mayar da dukiyar
  • Tuni dai jami'an yan sanda suka tafi da shi caji ofis domin gudanar da binciken kwa-kwaf da gurfanar da shi a gaban alkali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Wani fasto ya ki mayar da N900,000 da wanda ke zuwan cocinsa bauta ya tura masa bisa kuskure.

Fasto
Ana zargin fasto da cuwa cuwar makudan kudi. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Facebook

Fasto ya ji N1m, ya yi gum!

A wani faifayin bidiyo mai minti hudu da dakika 55 da Seun Adedara ta wallafa a shafinta na Facebook yan sanda sun kama faston.

Kara karanta wannan

'Banex Plaza': Soja ya shararawa wata mata mari har ta fada doguwar suma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin da yan sanda da suka ba faston damar yin bayani ya tabbatar da shigar kudin asusun bankinsa amma ya ce ba zai mayar da su ba.

Yadda aka tura wa Faston kudin

Faston ya labarta cewa mutumin ya za cocinsa ne a lokacin da suka neman taimako domin yin ayyuka na musamman.

Saboda haka sai ya nuna sha'awar tura gudunmawa domin neman lada, a maimakon tura N100,000 sai ya tura N1m bisa kuskure.

Mutumin ya yi kokarin kiran faston domin dawo masa da sauran kudin amma faston ya ki sai da aka kira jami'an yan sanda.

Dalilin Faston na kin mayar da kudin

A faifai bidiyon faston ya ce mutane suna ganin tura kudin kamar kuskure aka samu amma a badini ba kuskure bane.

Ya fadi haka ne saboda a cewarsa Allah ya san mutumin ya na da kudi sosai saboda haka sai aka matse hannunsa ya tura taimakon da yawa.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi:'Ka da gwamnati ta kuskura ta mana tayin N100,000,' TUC

Yan sanda sun ki amincewa da dalilin da faston ya bayar saboda haka suka tafi da shi domin zurfafa bincike duk da darajarsa.

Amma a lokacin da yan sanda ke tafiya da faston ya gargade su kan kar su kuskura su taba shi domin fushin Allah zai same su.

Fasto ya jawo ce-ce-ku-ce

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addini da ya yi busharar cewa za ayi tashin alkiyama a ranar, 25 ga Afrilu, 2024 ya jawo cece-kuce a soshiyal midiya.

A 'yan makonnin da suka gabata ne Faston ya yi iƙirarin cewa ya sami wahayi kan ranar busa kaho inda ya nemi kowa ya shirya tafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng