Shaye Shaye: Mahaifi Ya Bukaci Kotu Ta Daure Dansa a Jihar Kano

Shaye Shaye: Mahaifi Ya Bukaci Kotu Ta Daure Dansa a Jihar Kano

  • Wani mahaifi da ya nemi a boye sunansa ya shigar da dan cikinsa kara kotun shari'ar Muslunci da ke Fagge a jihar Kano
  • A zaman kotun, mai gabatar da kara Malam Abdul Wada ya bayyanawa wanda ake zargi laifuffukansa kuma ya amince
  • Bayan tabbatar sauraron jawaban mai kara da wanda ake kara, alkalin kotun, Mai shari'a Malam Umar ya dauki mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa wani mahaifi ya kai karar dansa kotun Muslunci da ke Fagge Yan Alluna a Kano.

Kano Kotu
Mahaifi na nemi a daure dansa saboda shaye-shaye. Hoto: Witthaya Prasongsin
Asali: Getty Images

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa mahaifin ya kai karar dan nasa ne saboda ya fitine shi da sace-sace da shaye-shaye.

Kara karanta wannan

NSCDC ta damke mai safarar mutane a Kano, wasu sun tsere

Hukuncin da mahaifin ya nema a yanke

Duk da cewa an boye sunan mahaifin a kotun, ya nemi a yanke wa dan hukuncin daurin rai da rai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai gabatar da kara a kotun, Abdul Wada ya karanta wa wanda ake kara abubuwan da ake zarginsa da su kuma ya amince da laifinsa.

Matakin da kotun ta dauka a kan yaron

Bayan sauraron jawabai daga wanda ake kara da mai shigar da kara, alkalin kotun, mai shari'a Umar Lawal Abubakar ya daga shari'ar.

Ana sa ran cigaba da sauraron shari'ar a gaban kotun ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni na wannar shekarar

An nemi gyara dokar masarautun Kano

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar KACDA, wacce ke rajin kare martabar al'adun jihar Kano, ta yi kira ga gwamnatin jihar, da ya rushe tsarin masarautu biyar

Kara karanta wannan

Rana dubu ta barawo: 'Yan sanda a jihar Niger sun yi ram da barayin ATM

Kungiyar ta nemi da a dawo da tsarin sarki ɗaya tilo a jihar domin dawo da martaba da kwarjinin masarautar Kano a idon duniya

EFFC ta bankado badakalar N2.17bn

A wani rahoton, kun ji cewa hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bankado badakalar da aka yi a lokacin shugaba Goodluck Jonathan.

Ana zargin badakalar ta faru ne karkashin ofishin mai ba shugaba Jonathan shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki (Mai ritaya).

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel