Kungiyar ASUU Ta Gudanar da Zanga Zanga, Ta Fara Haramar Yajin Aiki

Kungiyar ASUU Ta Gudanar da Zanga Zanga, Ta Fara Haramar Yajin Aiki

  • Kungiyar malaman jami'a ta kasa (ASUU) ta gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna fushi kan gwamnatin tarayya
  • A yayin gudanar da zanga-zangar a jihar Gombe, Farfesa Namo Aku Timothy ya bayyana bukatun kungiyar a wajen gwamnati
  • Legit ta tattauna da dalibin jami'a, Adamu Aliyu Abubakar kan jin yadda yajin aikin zai shafi karatun dalibai a manyan makarantu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Kungiyar malam jami'a ta kasa (ASUU) ta gudanar da zanga-zangan lumana domin neman gwamnati ta biya mata bukatun ta.

TINUBU
Kungiyar ASUU ta yi zanga zanga a jihar Gombe. Hoto: @OfficialABAT, @ridoradeola
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa kungiyar ta yi zanga-zangar ne a jami'ar jihar Gombe a jiya Talata.

Kara karanta wannan

Sarki 2 a lokaci 1: Lauyoyin Kano sun fitar da jawabi ganin an jibge jami'an Sojoji

Kungiyar ta ce tsawon shekaru 15 gwamnatin tarayya ta yi tana yaudarar ta kan alkawura da yarjejeniyar da suka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zanza-zangar ASUU a Gombe

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Namo Aku Timothy ya zantawa yan jarida dalilin fitowar su zanga a jihar Gombe.

Farfesa Timothy ya ce cikin manyan abin da suke buƙata gwamnati ta yi akwai biyansu alawus na tsawon shekaru.

Ya kara da cewa akwai albashinsu da gwamnati ta rike na wata uku da kuma bukatar cire su cikin tsarin biyan albashi ta manhajar IPPIS.

Farfesan ya kara da cewa tun a shekarar 2009 suka rattaba hannu kan alkawari da suka yi da gwamnatin tarayya amma har yau gwamnatin ta gaza cika alkawuran.

ASUU ta yi barazanar fara yajin aiki

Shugaban kungiyar ASUU na jami'ar Tafawa Balewa, Muhammad Muhammad Inti ya gargadi gwamnatin tarayya kan jinkirin biya musu bukatunsu.

Kara karanta wannan

Kotu ta raba gardama kan sahihancin zaben gwamnan APC, ta jero hujjoji

Malamin jami'ar ya ce matuƙar gwamantin ta gaza sauraronsu a wannan lokacin, za su tsunduma yajin aiki.

Legit ta tattauna da dalibin jami'a

Wani dalibin a jami'ar jihar Gombe, Adamu Aliyu Abubakar ya bayyanawa Legit cewa yajin aikin da ASUU ke shirin shiga zai zama barazana ga karatun dalibai a jami'o'i.

Saboda haka ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da gwamnatin tarayya kan daukan matakin da zai hana tafiya yajin aikin, musamman idan aka lura da halin matsin tattalin arziki da ake ciki.

ASUU ta gargadi gwamnatin tarayya

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta jima tana faɗi-tashin a kara yawan kasafin ilimi da kuma inganta walwalar 'ya 'yanta.

A ranar Talata, 21 ga watan Mayu, 2024 ASUU ta bayyana cewa za ta ayyana shiga yajin aiki kowane lokaci daga yanzu saboda biris da gwamnati tayi da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel