Kotu Ta Tube Rawanin Fitaccen Sarki a Najeriya, an Kwashe Shekaru 29 Ana Shari’a
- Wata babbar kotu a Najeriya ta tsige Oba Michael Adetunji Oluwole a matsayin Olute na Ute a Ondo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya
- Kotun ta kuma hana sarkin bayyana kansa a matsayin Olute na Ute, amma yana da zabin kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara
- Mai shari’a Ademola Enikuomehin ya ba da umarnin sake zaɓen wani sarkin daga cikin zuriyar Mai martaba Olule Omoloja a jihar Ondo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Owo, Ondo state - Wata babbar kotu ta tube rawanin basaraken Owo, Oba Michael Adetunji Oluwole, daga mukamin Sarkin Ute a karamar hukumar Ose (LGA) ta jihar Ondo.
An fara shari'ar Sarkin Ute a 1995
An ruwaito cewa Oba Michael Adetunji Oluwole ya shiga takaddamar shari'a game da zamansa sarki tun a shekarar 1995.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, gidan sarauta na Olule Omolaja ya kalubalanci cancantar babban sojan (mai ritaya) na samun damar hawa karagar mulki a masarautar.
A hukuncin da ya yanke kan karar da Adewumi Fabuluje ya shigar, Mai shari’a Ademola Enikuomehin, a ya soke tsarin zaben da ya dora Oba Oluwole kan karagar mulki.
Sarki Michael zai iya daukaka kara
Mai shari’a Ademola Enikuomehin ya kuma ba da umarnin a gudanar da sabon zaben sarki na masarautar, in ji rahoton FRCN.
Alkalin kotun ya umurci Oluwole da ya daina bayyana kansa a matsayin basaraken garin.
Mai shari'an ya kara da cewa za a zabi sabon sarki ne daga zuriyar Olule Omoloja kadai.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa, korarren sarkin yana da zabin kalubalantar hukuncin da babbar kotun ta yanke a kotun daukaka kara.
Za a gyara dokar Sarakunan Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar jihar Kano ta fara shirin gyara dokar Sarakunan Kano da Abdullahi Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Sarki Sanusi II a 2019.
Shugaban masu rinjaye kuma mai wakiltar mazabar Dala, Hussien Dala, ya gabatar da kudirin a gaban majalisar wanda aka amince da shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng