'Banex Plaza': Daga Karshe Sojoji Sun Bayyana Dalilin Kulle Babban Kantin Abuja

'Banex Plaza': Daga Karshe Sojoji Sun Bayyana Dalilin Kulle Babban Kantin Abuja

  • Daga ƙarshe rundunar sojojin Najeriya ta fito tayi magana kan dalilim da ya sanya aka kulle babban kantin 'Banex Plaza' da ke birnin tarayya Abuja
  • A wata sanarwa da kakakin rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ya bayyana cewa an rufe kantin ne domin gudanar da bincike kan ta'asar da aka yiwa sojoji
  • Ya bayyana cewa rufe kantin na wani ɗan lokaci ne domin zaƙulo ƴan daban da suka yiwa dakarun sojojin Najeriya aika-aika

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta yi magana kan rufe babban kantin 'Banex Plaza' da ke Abuja.

An kulle kantin ne tun bayan da wasu ƴan daba suka kai hari kan wasu sojoji a ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda 7, sun kwato makamai masu yawa a Kaduna

Dalilin sojoji na rufe Banex Plaza
Rundunar sojoji za ta yi bincike a Banex Plaza a Abuja Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar, ya ce an rufe kantin ne na wani ɗan lokaci, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rufe 'Banex Plaza' a Abuja?

Ya bayyana cewa an kulle kantin ne domin gudanar da bincike ta yadda za a zaƙulo ƴan daban da suka yi aika-aikar ta ranar Asabar.

Jaridar TheCable ta ambato wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Dangane da wannan mummunan lamari, an kira taro da mahukuntan Banex Plaza domin ganowa tare da damke wadanda suka aikata wannan ɗanyen aiki ta hanyar dakatar da harkokin da ake gudanarwa a kantin na wani ɗan lokaci."
"An yi hakan ne domin tabbatar da cewa ƴan daban da ke amfani da yankin 'Banex Plaza' a matsayin mafaka domin kawo barazanar tsaro a birnin tarayya an damke su."

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga yanayi yayin da ƴan bindiga suka kashe sojojin Najeriya

"Hakan ya nuna buƙatar gudanar da cikakken bincike a wurin domin gano dalilin da ya haddasa abubuwan da suka faru."
"Rundunar sojojin Najeriya za kuma ta gudanar da sahihin bincike kan abin da ya faru na zuwan sojoji babban kantin da kuma farmakin da aka kai musu daga baya."

Sojoji sun hallaka ƴan ta'adda

A wani labarin kuma kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasarar hallaka ƴan ta'adda bayan sun gwabza gagarumin artabu a jihar Kaduna.

Sojojin a yayin artabun sun hallaka ƴan ta'adda mutum bakwai tare ƙwato tarin makamai masu yawa daga hannun tsagerun masu addabar mutane.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel