Harin Masallacin Kano: Abba Ya Bayyana Hukuncin da Ya Ke Jira a Yanke Wa Mai Laifin

Harin Masallacin Kano: Abba Ya Bayyana Hukuncin da Ya Ke Jira a Yanke Wa Mai Laifin

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ziyarci masallatan da aka kona a wani masallaci da ke karamar hukumar Gezawa
  • Gwamnan ya ce zai rattaba hannu kan hukuncin kisa idan shi ne kotu za ta yanke wa wanda ya aikata laifin ba tare da jinkiri ba
  • Bayan ganawa tare da jajantawa wadanda iftila'in ya rutsa da su, mai girma Abba ya rabawa kowannensu kyautar kudi N100,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin hukunta wanda ya kulla fetur a leda, ya kona masallata a garin Larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya ziyarci mutanen da wannan iftila'in ya rutsa da su a asibitin kwararru na Murtala Muhammad, inda suke karbar magani.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

Gwamnan Kano ya yi magana kan harin masallacin Gezawa
Gwamna Abba zai goyi bayan hukuncin kisa ga wanda ya jefa bam a masallacin Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa, EngrAbbaKYusif
Asali: Facebook

Babban mai tallafawa gwamnan ta fuskar kafofin sada zumunta na zamani, Abdullahi I. Ibrahim ya wallafa bidiyon jawabin gwamnan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba zai rattaba hannu kan hukuncin kotu

Gwamnan jihar na Kano ya ce gwamnati da jami'an tsaro za su tabbatar an yi bincike kuma an gurfanar da mai laifin a gaban kotun Musulunci.

Gwamna Abba ya ce za a tabbatar an kwato hakkin wadanda ke kwance a asibiti da kuma wadanda suka riga mu gidan gaskiya.

Sannan Gwamnan ya ce zai sa hannu a kan hukuncin kisa da za a yanke wa wanda ya aikata laifin kone mutanen ba tare da jinkiri ba.

Abba ya tallafawa mutanen da suka kone

Sanarwar Abdullahi I. Ibrahim ta kara da cewa:

"Gwamnan, ya yi alkawarin bayar da duk wata gudunmowa da ake bukata domin ganin wadanda suka tsira daga harin sun samu lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta raba tallafin kayan noma a Kano domin magance yunwa

Da yake bayar da tallafin N100,000 ga kowanne majinyaci, gwamnan ya bayyana cewa kona masallatan ya samo asali ne daga rikicin rabon gado a tsakanin wasu ‘yan uwa."

Masallata 15 sun mutu a harin Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa akalla mutane 15 ne suka mutu a wani hari da wani matashi ya jefa masu a lokacin da suke tsakiyar gabatar da sallar Asubah a jihar Kano.

An ce mutane kusan 40 ne harin ya rutsa da su, kuma wadanda suka tsira daga harin na kwance a asibiti suna samun kulawa daga likitoci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel