InnalilLahi: An Samu Ƙarin Mutanen da Suka Mutu a Harin da Aka Kai Masallaci a Kano

InnalilLahi: An Samu Ƙarin Mutanen da Suka Mutu a Harin da Aka Kai Masallaci a Kano

  • Ƴan sanda sun tabbatar da cewa zuwa yanzu mutum 15 sun mutu sakamakon harin da aka kai masallaci ranar Laraba a Kano
  • Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya bayyana cewa ƴan sanda na kan bincike kan lamarin da ya auku a kauyen Gadan
  • Idan baku manta ba Shafi'u Abubakar, ɗan shekara 38 ne ya cinna wa mutanen wuta suna tsaka da sallar asubahi a makon nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni sun nuna cewa an ƙara samun waɗanda suka rasu daga cikin mutanen da harin masallaci ya rutsa da su a kauyen Gadan, ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa mutum 15 sun mutu sakamakon harin, wanda wani matashi ya bankawa masallaci wuta ana cikin sallah.

Kara karanta wannan

Dala vs Naira: Dalilin da ya sa ya kamata Tinubu ya kori gwamnan CBN da minista 1

Kwamishinan ƴan sandan Kano, Usaini Gumel.
Rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum 11 sakamakon harin Masallaci Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro maku cewa wanda ake zargin, Shafi'u Abubakar, ya yi wa masallacin wanka da man fetur, kana ya ƙulle ƙofofi sannan ya cinna wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, wannan mummunan lamari dai ya rutsa da mutane 40 a lokacin suna cikin sallar asubahi ranar Laraba da ta shige.

Kano: CP Gumel ya ce mutum 15 sun mutu

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Usaini Gumel, ya shaidawa hukumar dillancin labarai (NAN) cewa zuwa yanzu mutum 15 sun mutu daga cikin mutane 24 da suka samu raunuka.

Gumel ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da ake sallar asuba a wani masallaci da ke kauyen Gadan, inda mutane 24 suka jikkata.

Ya ce wadanda suka jikkata a halin yanzu su na kwance ana ba su kulawa a asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano.

Kara karanta wannan

Sama da mutum 10 sun mutu a harin da aka kai masallaci a Jihar Kano

Ƴan sandan Kano na tsare da Shafi'u

NAN ta ruwaito cewa wanda ake zargin, Shafi’u Abubakar, mai shekaru 38 a yanzu haka yana tsare hannun ‘yan sanda.

A cewarsa, ya ɗauki wannan matakin ne saboda zaluntar da aka masa a rabon gadon gidansu, shiyasa ya ƙona masallacin saboda waɗanda yake zargi suna ciki.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, rahoton Leadership.

Malam Sa'idu, mazaunin Kano ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan lamari ya. yi matuƙar tayar masu da hankali musamman kasancewar a Masallaci ɗakin Allah ya faru.

Ya ce ya samu zuwa asibitin da aka kwantar da waɗanda ibtila'in ya rutsa su amma abin da ya gani ya ɗaga masa hankali.

Ya ce:

"Addu'a kawai suke bukata amma suna cikin mawuyacin hali, babban abin tashin hankalin a masallaci aka cinna wuta a jihar Musulunci kamar Kano.

Kara karanta wannan

'Mutuwar' wani matashi Kabiru sakamakon azabtarwar ƴan sanda ya tada ƙura a Najeriya

"Mutum 15 ne suka rasu, an tabbatar mana cewa ƙarin mutum 4 sun cika da yammacin Alhamis, jimulla mutum 15 kenan idan aka haɗa da 11 da aka yi wa jana'iza, Allah ya jiƙansu."

Kotu ta hana belin jami'in Binance

A wani rahoton na daban, Babbar kotun tarayya ta yi watsi da buƙatar bayar da belin jami'in Binance, Tigran Gambaryan, saboda tunanin zai iya tserewa daga Najeriya

Mai shari'a Emeka Nwite ne ya yanke wannan hukunci yayin zaman ci gaba da shari'a kan tuhumar safarar kuɗin haram ranar Jumu'a a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel