'Mutane 4 aka Sace ba 500 ba,' DHQ ta yi Bayani kan Satar Mutanen Zamfara
- Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta karyata labarin cewa ‘yan ta’adda sun samu nasarar kutsawa karamar hukumar Zurmi tare da sace mutane 500
- Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa mutane 4 aka dauke a harin, wanda ya saba da adadin wadanda ake yadawa
- Tun bayan kai harin da bullar labarin ne shi ma Gwamnan Zamfara, Dauda Lawan Dare ya zargi wasu da ya kira makiya jihar da yada labaran karya kan harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara- Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta cewa mutane 500 yan bindiga su ka sace a jihar Zamfara.
Rahotanni sun karade kafafen yada labarai cewa 'yan ta'adda sun sace mutane kimanin 500 a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ya ce labarin kanzon kurege ake yadawa, kamar yadda Leadership News ta wallafa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zamfara: "Mutane 4 aka sace," DHQ
Hedkwatar tsaron kasar nan ta bayyana cewa mutane hudu 'yan ta'adda su ka ce a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.
Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan, sabanin mutane 500 da aka ruwaito tun da farko.
Ya ce dakarun operation hadarin daji na iya bakin kokarinsu wajen dakile hare-haren 'yan bindigar.
Gwamnan Zamfara ya karyata labarin
Tun bayan bullar labarin sace mutane kimanin 500 ne gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya musanta labarin sace mutane 500 a wata karamar hukumar da ke jihar, kamar yadda TVC News ta wallafa.
An dai fara yada wani labarin sace mutane 500 a yankin karamar hukumar Birnin Magaji, abin da Gwamnan ya zargi wasu da ya bayyana da makiya jihar Zamfara da yada labaran karya kan harin.
Ana neman Halilu Buzu Ruwa a jallo
Mun kawo mu ku labarin cewa rundunar sojojin kasar nan ta bayyana neman wani Halilu Buzu ruwa a jallo bisa zargin aikata laifin ta’addanci.
Rundunar ta ce yanzu haka ta na aiki da sojojin Nijar domin kama dan ta’addan da ya gawurta wajen kai hare-hare wasu yankunan Arewacin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng