Yan Sanda Sun Kama 'Dan Kasar Waje da Zargin Garkuwa da Mutane a Najeriya

Yan Sanda Sun Kama 'Dan Kasar Waje da Zargin Garkuwa da Mutane a Najeriya

  • Jami'an yan sanda sun kama mutane uku da ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Delta ciki har da wani dan kasar waje
  • Mutanen ana zarginsu ne da jagorantar ayyukan garkuwa da mutane a yankunan Orerokpe, Sapele da Warri na jihar Delta
  • Kakakin yan sandar jihar, Edafe Bright ya tabbatar da kama mutanen da kuma bayyana halin da ake cikin kan sauran da suka gudu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta -Jami'a tsaron farin kaya da ƴan sandan jihar Delta sun kama wani mutumin kasar Kamaru bisa zargin garkuwa da mutane.

Nigerina Police
Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutanen da suka fitini Warri. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Ana zargin mutumin ya yi haɗaka da wasu 'yan Najeriya su biyu wajen gudanar da ayyukan ta'addanci a jihar Delta.

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Karancin noma a Arewa na barazanar kawo matsalar abinci a Najeriya

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa daya cikin wadanda ake zargin dan asalin jihar Kaduna ne, daya dan asalin jihar Kogi sai dayan kuma ɗan ƙasar Kamaru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ake zargin mutanen a kai

Ana zarginsu da yin garkuwa da mutane da sauran ayyukan ta'addanci a yankunan Orerokpe, Sapele da Warri a jihar Delta.

Bayyanan sirri sun nuna cewa Yakubu Ya'u dan asalin jihar Kaduna yana zuwa yankin Oha da Ughwagba domin farautar mutane.

Idan ya je wuraren yana duba yadda mutane suke hada-hada daga nan sai ya yi garkuwa da su yana neman kudin fansa.

Yadda yan sanda suka kama su

Biyo bayan kama Yakubu Ya'u ne jami'an tsaro suka tsananta bincike har ya lissafo yan uwansa da suke aikin tare, rahoton jaridar Tribune.

Hakan kuma yasa aka kamo sauran wadanda ake zargin; Musa Yakubu daga jihar Kogi da Abdullahi Muhammad daga kasar Kamaru.

Kara karanta wannan

Yan ta'addan ISWAP da Boko Haram sama da 40 sun mika wuya a jihar Borno

Yan sandan jihar Delta sun yi karin haske

Jami'an yan sanda na jihar sun yi nasarar kwato makaman da mutanen ke aiki da su ciki har da bindiga biyu da wuka.

Kakakin yan sandan jihar, Edafe Bright ya sanar da cewa yanzu haka ana bincike domin kamo sauran wadanda suka gudu daga cikinsu.

An yi garkuwa da malamin addini

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban malamin addinin Kirista a jihar Anambra, inda aka bazama neman su ba tare da nasara ba.

Shugaban cocin Katolika na Onitsha, Prudentius Aroh, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa an dukufa yin addu’a domin ceto malamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng