Shugaba Tinubu Ya Amince da Biyan Bashin Maƙudan Tiriliyoyin Kuɗi da Ake Bin Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Amince da Biyan Bashin Maƙudan Tiriliyoyin Kuɗi da Ake Bin Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin biyan bashin kuɗaɗen da ake bin ɓangaren wutar lantarki wanda ya haura N3.3trn
  • Shugaban ƙasar ya amince a biya bashin a hankali a hankali domin magance matsalar rashin samun wutar lantarki a ƙasar nan
  • Ministan makamashi, Adebayo Adeabu ne ya bayyana haka a wurin wani taro na nahiyar Afirka da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da biyan bashin da ake bin ɓangaren wutar lantarki wanda aka yi ƙiyasin ya kai sama da N3.3tn.

Bola Tinubu ya ɗauki matakin biyan basussukan da ake bin ɓangare ne a wani yunƙuri na magance matsalar rashin wutar lantarki a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Ana murnar Notcoin ya fashe, kotun tarayya ta yanke hukunci kan jami'in Binance a Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara biyan wasu basussuka da ya gada a gwamnati Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya za ta rage bashin wuta

Bisa haka gwamnatin tarayya za ta biya kimanin N1.3trn wanda kamfanoin samar da wutar lantarki ke bi bashi ta hanyar amfani da tsabar kuɗi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan kuma za a biya kamfanonin iskar gas $1.3bn (watau N1.9trn a farashin musaya na yanzu) da tsabar kuɗi da kuma wasu kuɗin shiga nan gaba, Punch ta ruwaito.

Yadda gwamnatin Tinubu za ta biya bashin

Tuni dai gwamnatin tarayya ta fara biyan kashin farko na bashin N1.3tn da Gencos ke binta sannan ta kammala shirin warware kashi na biyu na bashin cikin shekara biyu zuwa biyar.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a taron makamashi na nahiyar Afrika karo na takwas da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Gwamnatin tarayya dai tana tallafawa ɓangaren wutar lantarki a Najeriya ta hanyar ɗaukar nauyin biyan kudin iskar gas don samar da wutar lantarki

Kara karanta wannan

Dala vs Naira: Dalilin da ya sa ya kamata Tinubu ya kori gwamnan CBN da minista 1

Amma a tsawon shekaru an daina biyan kuɗaɗen, wanda ya jawo tarin bashin iskar gas da kuma tarawa kamfanonin samar da wutar lantarki bashi mai nauyi.

Tinubu ya umarci a cire N130bn

Domin warware waɗannan basussuka, Adelabu ya ce tuni Bola Tinubu ya umarci ministan kuɗi ya biya N130bn domin rage bashin N1.3trn da Gencos ke bi.

Ministan ya bayyana cewa gwamnati za ta biya sauran bashin a hankali a hankali nan gaba.

Ya ƙara da cewa za a biya bashin $1.3bn da kamfanonin samar da gas ke bi da kuɗin shigar da gwamnati ke sa ran samu a ɓangaren gas nan gaba, Daily Post ta ruwaito.

Adelabu ya mayar da martani

A wani rahoton kuma ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya caccaki masu sukar gwamantin tarayya kan karin kudin lantarki ga 'yan sahun Band A.

Ministan ya ce maganar cewa karin kudin wutar ya jawo tashin kudin kayan masarufi magana ce da ba za ta kama hankali ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262