Mutane Sama da 10 Sun Mutu a Harin da Aka Kai Masallaci a Jihar Kano

Mutane Sama da 10 Sun Mutu a Harin da Aka Kai Masallaci a Jihar Kano

  • Mutum 11 sun kwanta dama sakamakon harin da wani matashi ya kai masallaci ana tsaka da sallar asubahi a jihar Kano jiya Laraba
  • Mazauna garin sun tabbatar da cewa an yi wa mutum takwas jana'iza kuma ana shirin ƙara kai wasu 3 makwancinsu yau Alhamis
  • Wani matashi, Shafi'u Abubakar ya cinna wa mutane wuta da safiyar ranar Laraba kana ya miƙa kansa ga ƴan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Rahotanni sun nuna cewa an tabbatar da nutuwar mutun 11 kawo yanzu sakamakon harin da wani matashi ya kai masallaci a jihar Kano.

Idan baku manta ba, Shafi'u Abubakar, ɗan kimanin shekara 38 a duniya ya bankawa wuta a wani masallaci a lokacin jama'a ke sallar Asubahi ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Mutane sama da 20 sun sutu a harin 'bam' da aka kai masallacin Kano

CP Usaini Gumel na Kano.
An tabbatar da mutuwar mutum 11 a harin da aka kai masallaci a Kano Hoto: Kano Police Command
Asali: Twitter

Akalla mutum 40 ne ke cikin masallacin sa'ilin da mutumin ya cinna wuta kuma ya rufe ƙofofi domin toshe masu hanyar tsira a yankin ƙaramar hukumar Gezawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani wani mazaunin kauyen Gadan, Rabiu Gadan, ya shaidawa jaridar Leadership cewa kawo yanzu mutum 11 sun rasu sakamakon ƙunewar da suka yi a harin.

Kano: An yi wa mamatan jana'iza

Ya ce tuni aka yi wa mutum takwas daga cikin Jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada yayin da sauran uku kuma za a masu jana'iza yau Alhamis.

Rabi'u ya bayyana cewa wannna harin ba shi ne laifi na farko da Shafi'u ya aikata ba domin ya taɓa azabtar da ƴan uwansa biyu kuma ya miƙa kansa ga ƴan sanda, ya yi iƙirarin ya kashe su.

Lafiya kalau matashi ya cinna wuta?

Wani mazaunin garin Malam Garba ya ce:

Kara karanta wannan

"Kano ta kama hanyar kamawa da wuta," Jigo ya buƙaci Tinubu ya dakatar da Gwamna Abba

"A ko da yaushe shi (Shafi'u) ba ya ƙaunar zaman lafiya, haka kurum ya ta da rigima a gidansu cewa a raba gado a ba shi kason shi, kuma suka raba suka ba shi.
"An taɓa kai shi asibitin mahaukata saboda ya farmaki ƴan uwansa amma daga bisani suka ce lafiyar kwankwalwarsa kalau.
"Saboda haka yana cikin hankalinsa lokacin da ya cinna wutar, biyu daga cikin kawunnansa sun mutu kuma mun masu jana'iza jiya."

Yanzu haka dai wanda ya aikata wannan laifin yana tsare a hannun ƴan sanda ana ci gaba da bincike.

Sojoji na neman Halilu Buzu ruwa a jallo

A wani rahoton kuma sojojin Najeriya sun bayyana Halilu Buzu a matsayin wanda suke nema ruwa a jallo bisa zargin aikata miyagun laifukan ta'addanci.

Bayanai sun nuna cewa Halilu, wanda ya tara yara a dajin Zamfara ya tsallake zuwa ƙasarsa ta haihuwa watau jamhuriyar Nijar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262