Shugaban APC Ganduje zai Sarara Bayan Kotu ta Dakatar da Bincikensa

Shugaban APC Ganduje zai Sarara Bayan Kotu ta Dakatar da Bincikensa

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta dakatar da bincikar tsohon Gwamna kuma shugaban jam'iyyar APC a yanzu Abdullahi Umar Ganduje
  • Tun da fari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya kafa wasu kwamitoci guda biyu domin binciken Ganduje kan zargin almundahana da rikicin siyasa
  • Duk da kwamitocin sun fara zama, mai shari’a Simon Amobede ya dakatar da kwamitocin har sai an kammala sauraron karar da Ganduje ya shigar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta dakatar da binciken da gwamnatin Kano ke yiwa tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan almundahana.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnan PDP ya ɗauki zafi, ya sha alwashin bincikar Ministan Bola Tinubu

Tun da farko, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kafa kwamitoci guda biyu domin bincikar yadda Abdullahi Ganduje ya gudanar da gwamnatinsa.

Abdullahi Umar Ganduje
Kotu ta haramta ci gaba da binciken Abdullahi Umar Ganduje Hoto: @tudunwada_mi
Asali: Twitter

Sauran aikin kwamitocin ya kunshi duba kan rikicin siyasar da aka samu a kakar zaben 2023, da kuma bacewar wasu mazauna jihar a tsakanin shekarar 2015-2023, kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun, karkashin jagorancin mai shari’a Simon Amobeda ta hana ci gaba da binciken har sai an kammala sauraron karar da shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya shigar gabanta.

Kwamitin binciken Ganduje ya fara zama

Kafin shigar da kara gaban kotu da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi ya na kalubalantar bincikensa da ake yi, tuni kwamitocin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa suka fara zama.

Kwamitocin da ke karkashin jagorancin Cif joji a Kano, Zuwaira Yusuf da Faruk Lawan sun yi zama domin fara binciken mulkin Ganduje, kamar yadda Pucnh News ta wallafa.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Sauran wadanda Dr. Ganduje ke kara sun hada da shugabannin kwamitocin da babban lauyan gwamnatin jihar, da hukumar tattara kudaden shiga da hukumar kasafin kudi da kuma majalisar shari’a ta kasa (NJC).

Mai shari’a Simon Amobeda da ya haramtawa kwamitocin binciken ya sanya ranar 28 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraren karar.

Za a fara sauraran karar Ganduje

A baya mun kawo muku labarin cewa babbar kotun tarayya a Kano ta sanya ranar fara sauraron karar da shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje ya shigar.

Kotun ta sanya ranar 28 ga watan Mayu domin fara sauraron karar da Ganduje ya shigar ya na kalubalantar korarsa da wasu ‘yan jam’iyyar APC su ka ce sun yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel