Gwamna Buni Ya Naɗa Sabon Sarki a Masarautar Tiƙau Bayan Ibn Grema Ya Rasu

Gwamna Buni Ya Naɗa Sabon Sarki a Masarautar Tiƙau Bayan Ibn Grema Ya Rasu

  • Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya naɗa Abubakar Muhammadu Ibn Grema a matsayin sabon sarkin Tikau bayan rasuwar mahaifinsa
  • A wata sanarwa da SSG na Yobe ya fitar, ya ce gwamnan ya amince da naɗin ne bayan masu naɗa sarki a masarautar sun miƙa masa shawarwarinsu
  • Wannan naɗi na zuwa ne bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Tikau a makon da ya gabata bayan ya sha fama da jinya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya naɗa babban ɗan marigayi Sarkin Tiƙau, Abubakar Muhammadu Ibn Grema a matsayin sabon sarkin masarautar.

Gwamna Buni ya naɗa sabon Sarkin Tikau ne biyo bayan rasuwar Mai Martaba Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na tunanin kwashe kuɗin ƴan fansho ta yi wasu muhimman ayyuka

Gwamna Mai Mala Buni.
Masarautar Tikau a jihar Yobe ta yi sabon sarki Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Baba Malam Wali, sakataren gwamnatin jihar Yobe ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Talata, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Gwamnan ya amince da naɗin sabon sarkin ne bisa la'akari na shawarin masu alhakin naɗa sabon Sarki a masarautar Tikau.

Taƙaitaccen bayani kan sabon Sarkin Tikau

Sabon Sarkin ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arzikin noma a Jami’ar Bayero da ke jihar Kano.

Haka nan kuma ya kammala digiri na biyu a wannan fanni yayin da yanzu haka yake ƙoƙarin haɗa digirin digirgir watau digiri na uku.

Sabon Sarkin ya yi aiki a kungiyoyi da dama da wurare daban-daban ciki har da Jami’ar Jihar Yobe da ke birnin Damaturu.

Yayin zamansa a makarantar ya riƙe manajan gonar jami'ar jihar Yobe har zuwa yau da aka naɗa shi sabon Sarkin Tiƙau.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnan PDP ya ɗauki zafi, ya sha alwashin bincikar Ministan Bola Tinubu

Muhammadu ya samu horo daban-daban a ciki da wajen kasar nan a fannin da ya yi karatu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Buni ya cire ciyamomi

A wani rahoton na daban gwamnatin jihar Yobe ta sanar da cewa ta rusa dukkanin shugabannin riko na kananan hukumomi 17 da da kansilolinsu.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar zabe ta jihar Yobe (YSIEC) ta sanya ranar 25 ga watan Mayu domin gudanar da zaben ciyamomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel