Kano: Sanata Hanga Ya Yi Karin Haske Kan Dalilin Rabon Kayan Gawa a Makabartu

Kano: Sanata Hanga Ya Yi Karin Haske Kan Dalilin Rabon Kayan Gawa a Makabartu

  • Sanatan Kano ta tsakiya, Rufa'i Hanga ya yi karin haske kan kayayyakin da ya raba a makabartu da ke cikin mazabarsa
  • Rufa'i Hanga ya bayar da dalilai kan raba tallafin tare da cewa yana fatan ya mutu a kan irin ayyukan domin samun rahamar Allah
  • Martanin da sanatan ya yi ya biyo bayan caccaka da masu amfani da kafafen sada zumunta suka yi ne a lokacin da ya raba kayayyakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Sanatan mai wakiltar mazabar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai, Rufa'i Hanga ya yi karin haske kan kayayyakin da ya raba a makabarta.

Sanata Hanga
Sanata Rufa'i Hanga ya ce ya raba tallafi a makabarta ne domin Allah. Hoto: Senator Rufa'i Hanga
Asali: Facebook

Kano: Kayayyakin da Sanata Hanga ya raba

Kara karanta wannan

Sankara: Kwamishina ya magantu kan zarginsa da Hisbah ke yi, ya fadi matakin gaba

A satin da ya wuce ne sanatan ya raba tukwanen kasa 2,000 da likkafani yadi 10,500 a wata makabarta da ke mazabarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai tallafi da sanatan ya bayar ya tayar da kura inda al'umma da dama suka soke shi.

Sai dai jaridar Leadership ta ruwaito cewa ya yi karin haske kan lamarin domin wanke kansa daga zargi.

Karin hasken da Sanata Hanga ya yi

Yayin da yake karin hasken ya bayyana cewa tallafin ya yi shi ne da kudin aljihunsa ba da kudin gwamnati ba.

A cewarsa, dukkan kayan da ya kai makabartar ya kaisu ne domin mutumta dan Adam idan ya mutu da kuma neman lada.

Sanata Hanga ya ce lalle ya gaji irin ayyukan ne wurin iyaye da kakanni kuma yana fatan cigaba da su har karshen rayuwarsa.

Wuraren da Hanga ya raba kayayyakin gawa

Kara karanta wannan

'Ana shan wuya,' Wani babba a APC ya cire kunya ya koka kan mulkin Tinubu

Kayayyakin dai an raba su ne ga ƙananan hukumomi 15 cikin mazabun da sanatan yake wakilta a Kano ta tsakiya.

Wanda hakan ne ya jawo cece-ku-ce a kafafen sadarwa kuma ya tilasta masa yin karin haske kan lamarin, rahoton Daily Post.

"Fa'idar raba kayan gawa" - Sanata Hanga

Dangane da muhimmancin aikin kuma, Sanata Hanga yace tukwanen suna da amfani sosai wurin kiyaye mamata da aka binne a makabartu.

Sannan ya kara da cewa ya raba tallafin ne biyo bayan taimako da kwamitin lura da makabartu na jihar Kano ya nema.

Kotu ta tabbatar da nasarar sanata Hanga

A wani rahoton kun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓe mai zamanta a birnin Kano ta yanke hukunci a kan ƙarar A. A Zaura da Sanata Rufa'i Hanga.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da A.A Zaura ya shigar inda ta tabbatar da Hanga dan jam'iyyar NNPP a matsayin zaɓaɓɓen sanatan Kano ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng