"Daurarru 400 a Kano ba su San Makomarsu a Gidan Yari ba," Inji 'Yan Sanda
- Kimanin mutane 400 ne da ke zaune a gidan gyaran hali da tarbiyya na Kurmawa a jihar Kano ba su san halin da shari'arsu ke ciki a gaban kotu ba
- Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki ranar Litinin a jihar
- Ya ce takardar tuhumar wasu daga daurarrun sun bata, sannan rashin masu bayar da shawara kan harkokin shari’a kyauta na kara ta’azzara lamarin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano-Daurarru kimanin 400 ne a jihar Kano ke tsare a gidan yarin kurmawa ba tare da sun san makomarsu ba.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin taron masu ruwa da tsaki da kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta shirya a jihar.
Vanguard News ta wallafa cewa da yawa daga daurarrun ba su san ina aka kwana kan tuhumar da ake musu ba saboda takaddun tuhumar sun bata bat, da kuma rashin lauyoyin da za su wakilce su, da kuma wasu da kotu ta ki bayar da belinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma ya bayyana karancin lauyoyi ko kwararru a fannin shari’a masu taimakawa kyauta ga wadanda ke dauren.
“Babu ban-dakuna a gidan yari,” CP Gumel
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel ya bayyana damuwa kan yadda daurarru ke zaune a gidajen yarin kuramawa a Kano babu kulawa.
Ya ce babu abubuwan tafiyar da rayuwa irinsu bandakuna, ko ofishin kula da lafiyar daurarrun, kamar yadda Peoples Gazette ta wallafa.
Haka kuma kwamishinan ya bayyana damuwa ganin babu ofishi mai kyau na jami’an gidan yarin, ko makaranta a cikin gidan kula da yara da ake zargi da laifuka a ajiye gidan gyaran hali na Goron Dutse.
CP Gumel ya ce wannan ya sanya rundunar ta samar da kwamitin da zai sanya idanu kan daftarin tsarin lauyoyin ‘yan sanda don rage matsalolin.
Akwai cunsoko a gidan yarin Kano
Mun kawo muku labarin cewa hukumar kula da gidajen gyaran hali da tarbiyya reshen Kano ta koka kan cunkoson da ake fuskanta a gidan yarin jihar.
Kakakin hukumar, Musbahu Lawan ne ya lamarin, inda ya kara da cewa kashi 70% na daurarrun na zaman jiran shari’a ne.
Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng