Kotu Ta Hukunta Matashi Mai Karyar Ya Shigo Musulunci Daga Kiristanci a Kano
- Wata kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a ƙaramar hukumar Kura a jihar Kano ta hukunta wani matashi mai ƙoƙarin ci da addini
- Kotun ta umarci a yi wa matashin bulala 10 bayan ta same shi da laifin yin ƙaryar cewa shi sabon musulunta ne yana karɓar sadaka a wajen mutane
- Matashin ya bayyana cewa ya yi nadamar wannan aikin da ya aikata tare da alƙawarin cewa zai koma makaranta ya ƙara karatun addini wajen malamai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Wata kotun Shari’ar Musulunci ta jihar Kano da ke zamanta a Kura, ta bayar da umarnin a yi wa wani matashi mai suna Haruna Abdulkarim ɗan shekara 25 bulala 10.
Kotun ta ba da umarnin ne domin ladabtar da shi bisa zarginsa da yin ƙaryar cewa shi Kirista ne wanda ya musulunta.
Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa jami’an hukumar Hisbah a ƙaramar hukumar Kura ne suka kama matashin, wanda ke zaune a unguwar Koguna da ke ƙaramar hukumar Makoda a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kasance yana halartar masallatai inda yake ƙaryar cewa shi Kirista ne mai son musulunta daga nan sai ya nemi sadaka.
Wannan yaudarar da yake yi ne ya sanya kwamandan Hisbah na ƙaramar hukumar Kura Ali Alkasim Kura ya ba da umarnin kama shi tare da miƙa shi ga ƴan sanda domin gudanar da bincike.
Meyasa matashin ya aikata laifin?
Daga baya an gurfanar da shi a gaban kotu inda ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, tare da bayyana cewa basussukan da suka yi masa yawa ya sanya ya ɗauki wannan hanyar mara ɓullewa.
Sai dai ya roƙi a yi masa sassauci, inda ya sha alwashin ba zai sake aikata irin wannan yaudarar ba, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Kotun dai ta yanke masa hukuncin bulala 10 tare da gargaɗin cewa idan ya sake aikata laifin zai samu hukunci mai tsauri.
Bayan zaman kotun Abdulkarim ya roƙi gafarar dukkan musulmi musamman waɗanda suka ba shi sadaka. Ya tabbatar da cewa ba zai sake aikata wannan aikin ba.
Da yake nuna ya yi nadama ta gaskiya, ya bayyana aniyarsa ta komawa wajen malaman addinim musulunci domin zurfafa fahimtar addininsa.
Kotu ta raba auren wasu ma'aurata
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta raba auren da ke tsakanin wani direba, Zakari Ghali, da Shamsiyya Haruna kan dalilin rashin zama wuri ɗaya.
Tun da farko Shamsiyya Haruna da ke zama a Unguwa Uku Quarters a jihar Kano ta shigar da ƙara gaban kotun Musulunci, inda ta roƙi alkali ya raba auren da ke tsakaninta da mijinta.
Asali: Legit.ng