Kakakin Majalisar Jihar Niger Zai Aurar Da Marayu 100

Kakakin Majalisar Jihar Niger Zai Aurar Da Marayu 100

  • Kakakin majalisar jihar Niger, Abdulmalik Sarkindaji ya bayyana shirin aurar da 'yan mata marayu 100 a mazabarsa
  • Shugaban ya sanar da cewa ya kammala dukkan shirye-shiryen auren tare da alkawarin biyan sadaki ga angwayen
  • A hirar da ya yi da ƴan jarida ya bayyana ranar da za a daura auren da manyan bakin da za su halarci bikin daga fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Niger - Kakakin majalisar dokokin jihar Niger, Abdulmalik Sarkindaji ya bayyana kudurin aurar da 'yan mata marayu 100.

kakakin majalisa
Kakakin majalisar jihar Niger zai aurar da 'yan matan da aka kashe iyayensu. Hoto: Abdulmalik Sarkindaji
Asali: Facebook

A cewar sanarwar, 'yan matan da zai aurar za su kasance ne cikin wadanda aka kashe iyayensu saboda rikicin 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

N15tr: "Za mu binciki yadda aka ba da kwangilar titin Lagos-Calabar", Majalisa

Rahoton jaridar the Nation ya nuna cewa za a yi auren ne ga ƴan matan da suka fito daga mazabar shugaban majalisar, ƙaramar hukumar Mariga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a daura auren?

Rahotanni sun nuna cewa za a yi auren ne a ranar Jumu'ah, 24 ga watan Mayu na wannar shekarar, cewar jaridar Punch.

Dadin dadawa kakakin majalisar ya sanar da cewa ya kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da bikin.

Ya kuma kara bada tabbacin cewa bikin zai samu armashi kamar sauran bukukuwa kuma za a yi shi ne bisa koyarwar addinin Muslunci.

Yan matan su 100 da suka samu shiga cikin auren an zabe su ne cikin mata 170 da aka tura sunayensu domin tantancewa.

Menene dalilin yin auren?

A yayin da yake zantawa da manema labarai a garin Minna, kakakin majalisar ya tabbatar da cewa bikin zai kasance cikin ayyuka na musamman da zai gabatar a mazabarsa.

Kara karanta wannan

Makiyayi ya datse hannun manomi saboda ya hana shi shiga gona a Kaduna

Ya kuma kara da cewa ya dauki nauyin bukukuwan ne domin rage radadin talauci da al'ummar Najeriya ke ciki a halin yanzu.

Manyan bakin da za su halarci bikin

Wani abin da ake sa ran zai karawa lamarin kima shine gwamnan jihar Niger ne, Muhammad Umar Bago da sarkin Kwantagora, Alhaji Muhammad Barau za su kasace waliyan ƴan matan.

Kuma ana san ran kwamandan Hisba na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai kasance cikin manyan baki da za su shaida daurin auren.

Za a sake auren zauarawa a Kano

A wani rahoton kuma, kun ji cewa hukumar Hisba ta jihar Kano ta fara shirye shiryen auren zawarawa karo na biyu a mulkin Abba Kabir Yusuf.

Kwamandan rundunar ne, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana lamarin yayin hira da manema labarai tare da bayyana sababbin tsare-tsare da suka kawo wannan karon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel