"Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 135, Ceto Mutum 140 da Aka Sace", DHQ

"Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 135, Ceto Mutum 140 da Aka Sace", DHQ

  • Dakarun sojojin Najeriya masu yaƙi da ta'addanci sun samu nasara gagaruma kam ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya a ƙasar
  • A cikin mako guda sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 135 tare da kuɓutar da mutim 140 da aka yi garkuwa da su a sassan daban-daban
  • Sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa da kuɗade tare da cafke 182 da ake zargi da aikata laifuffuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya da ke gudanar da ayyukan cikin gida a faɗin ƙasar sun yi nasarar kashe ƴan ta'adda 135 a cikin mako guda.

Dakarun sojojin sun kuma cafke mutum 182 da ake zargi yayin da suka kuɓutar da mutum 140 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya nuna babban kuskuren Tinubu kan harajin tsaron yanar gizo

Sojojo sun hallaka 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun hallaka 135 a cikin mako guda Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a 10 ga watan Matun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa dakarun sojojin sun kuma kama wasu mutum 15 da ake zargin barayin man fetur ne tare da ƙwato kayayyakin sata da suka kai N731,448,262.00, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Sojoji sun ƙwato makamai

Edward Buba ya ce sojojin sun ƙwato makamai iri-iri guda 97 da alburusai iri-iri guda 3,117.

Daraktan ya ce sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda tare da rage ƙarfin da suke da shi wanda hakan ya sanya da yawa suka sheƙa zuwa barzahu.

Makaman da aka ƙwato sun haɗa da bindigu guda 47 ƙirar AK-47, bindiga ɗaya ƙirar PKM MG, bindigar ƙirar FN guda ɗaƴa, bindigogi ƙirar guda 17, bindigu 21, manyan bindigu guda 9, ƙananan bindigu ƙirar gida guda uku, gurneti 36 da bam ɗaya.

Kara karanta wannan

An ƙara yi wa dakarun sojoji sama da 20 kisan gilla a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Sauran abubuwan da aka ƙwato sun haɗa da harsasai na musamman masu kaurin 7.62mm guda 1,087, harsasai na musamman na NATO masu kaurin 7.62mm guda 840, harsasai guda 402 masu kaurin 7.62mm.

Sauran su ne harsasai 88 masu kaurin 5.56mm, harsasai 33 masu kaurin 9mm, harsasai 90, jigida 29, ababen hawa 15, babura 21, kekuna guda shida, wayoyi 43 da zaɓar kuɗi N2,024,210.00.

Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun daƙile wani yunƙurin ƴan ta'adda na yin garkuwa da mutane a jihar Benue.

Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun ceto wasu mutum biyu da aka so a yi garkuwa da su zuwa cikin daji a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng