Bakuwar Cuta Ta Bulla a Zamfara, an Rasa Rayukan Bayin Allah

Bakuwar Cuta Ta Bulla a Zamfara, an Rasa Rayukan Bayin Allah

  • An samu bullar wata baƙuwar cuta wacce har yanzu ba a san musabbabinta ba a wasu ƙananan hukumomi guda uku na jihar Zamfaran Najeriya
  • Kwamishiniyar lafiya ta jihar wacce ta tabbatar da ɓullar cutar ta bayyana cewa an samu asarar rayukan mutum huɗu yayin da ta kama mutum 177
  • A cewar cutar wacce kwamishiniyar an ɗauki samfuri domin gudanar da gwaje-gwaje waɗanda za su bayyana haƙiƙanin ko wace irin cuta ce

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wata baƙuwar cuta ta yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu tare da shafar mutum 177 a jihar Zamfara.

Kwamishiniyar lafiya ta jihar Dr Aisha Anka ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar, Malam Bello Ibrahim ya fitar a Gusau ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya nuna babban kuskuren Tinubu kan harajin tsaron yanar gizo

Bakuwar cuta ta bulla a Zamfara
An samu bullar bakuwar cuta a Zamfara Hoto: @Mfareees
Asali: Twitter

A cewar kwamishinan, cutar na da nasaba da kumburin ciki, tara ruwa a cikin ciki, ƙara girman hanta, ƙara girman hanji, zazzaɓi, da raunin jiki gaba ɗaya, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ina cutar ta ɓulla?

Cutar an same ta ne a ƙananan hukumomi uku na jihar da suka haɗa da Maradun, Shinkafi da Gusau.

Ta bayyana cewa hukumar ta duƙufa wajen ganin ta gano musabbabin ɓarkewar cutar, rahoton Radio Nigeria ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“An gano cutar a ƙananan hukumomin Maradun, Shinkafi, da Gusau. Ta fi shafar yara kuma cutar tana da alaƙa da shan ruwa."
"Ya zuwa yanzu, an sami rahoton mutuwar mutum hudu, kuma an gano ta kama mutum 177. An kai rahoton faruwar lamarin ga hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa (NCDC), da abokan huldar ta, da duk sauran masu ruwa da tsaki."

Kara karanta wannan

Wata cuta ta kashe ɗalibai 6 na makarantar Alƙur'ani Mai Girma a Bauchi

"An kai samfuri iri-iri na mutane da na dabbobi, na ƙasa, ruwa, noma da kayan abinci ɗakunan gwaje-gwajen Legas da Abuja domin yin bincike."

Baƙuwar cuta ta ɓulla Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta NCDC ta tabbatar da ɓullar wata baƙuwar cuta a jihar Sokoto.

Hukumar ta ce ba a san asalin cutar ba, kuma zuwa yanzu mutum huɗu sun rasu sakamakon ɓarkewar cutar wacce ake zargin ta kama mutum 164.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng