Matasan Arewa Sun Taso Sanata Ali Ndume a Gaba Kan Wasu Kalamai a Majalisa
- Wata ƙungiyar matasan Arewa ta caccaki Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu saboda kalaman kan gyaran da aka yi wa majalisar tarayya
- Sanata Ndume a kalaman da ya yi ya koka da cewa muhimman abubuwa ba su aiki a majalisar duk kuwa da gyaran da aka yi wanda ya lashe biliyoyin kuɗaɗe
- Kungiyar ta ce kamata ya yi Sanatan ya mayar da hankali kan abubuwan da suka damu al'ummar Najeriya ba ƙaramin abu ba kamar wannan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar matasan Arewa NEYGA, ta yi kira Sanata Ali Ndume, da ya mayar da hankali kan babban dalilin da ya sa yake cikin majalisar dattawa.
Ƙungiyar ta caccaki Sanata Ali Ndume saboda surutun da ya yi kan rashin aikin wasu muhimman abubuwa a zauren majalisar da aka gyara.
Wace shawara aka ba Sanata Ali Ndume?
Daga nan sai suka shawarce shi da ya mayar da hankali kan wani abu mai ma’ana da ya shafi al’ummar ƙasa baki daya, suna masu cewa za a iya warware matsalar majalisar dattawa a cikin gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan caccakar dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar, Ibrahim Dan-Musa ya fitar a ranar Alhamis, 9 ga Mayun 2024, cewar rahoton jaridar Leadership.
Ƙungiyar ta ce kamata ya yi majalisar dattawa ta yi koyi da irin ayyukan da Majalisar Wakilai ke yi, inda suka mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi ƙasa baki ɗaya, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Muna shawartar shugabannin majalisar dattawa da su yi koyi da dattako da kamala irin na takwarorinsu a majalisar wakilai domin majalisar dattawa cibiya ce ta yin dokokin da suka dace da sa ido kan gwamnati."
Zaɓin Ndume tsakanin Buhari da Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya bayyana bambancin da ke tsakanin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta Shugaba Muhammadu Buhari da ta shuɗe.
Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce ba Buhari ne ke gudanar da gwamnatinsa ba, saboda ba ya bibiyar ayyukan da ya ba mutanen da ya naɗa muƙamai.
Asali: Legit.ng