'Yan Bindiga: Majalisa Ta Bukaci Samar da Jami’an Tsaron Hadin Gwiwa a Niger
- Majalisar wakilai ta fara duba yiwuwar kafa jami'an tsaro na musamman a jihar Niger saboda yawaitar ayyukan ta'addanci
- Dan majalisa, Isma'ila Musa Modibbo ne ya kawo kudurin tare da ayyana yankunan da suka fi bukatar samun jami'an cikin gaggawa
- Ya kuma bayyana dalilan da suka sa ya yi kiran a wannan lokacin ta hanyar bayani kan asarar da ake tafkawa a yankunan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Majalisar wakilai ta yi kira na musamman domin samar da jami'an tsaro na hadin gwiwa domin magance matsalolin 'yan bindiga a jihar Niger.
Kiran ya zo ne a daidai lokacin da miyagun 'yan bindiga dadi, masu garkuwa da mutane da sauran 'yan ta'adda suka yawaita kai hare-hare a jihar.
Yankunan Niger da za a saka jami'an tsaro
Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya yi nuni da cewa majalisar ta nemi karin jami'an tsaron ne a yankunan Shiroro, Rafi da Munya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan majalisar wakilai, Isma'ila Modibbo ne ya kawo kudurin a majalisar yayin da suke tattaunawa a jiya Laraba, 8 ga watan Afrilu.
Dalilin majalisa na samar da jami'an tsaro
A cewar dan majalisar, yankunan sun dade suna fama da hare-haren 'yan bindiga a kai-a kai, cewar jaridar Daily Nigerian.
Sanadiyyar ayyukan 'yan bindiga a yankunan, rayuka da dama sun salwanta, wasu an sace su, wasu kuma an lalata musu gidaje da gonaki.
Ya kara da cewa hare-haren sun kuma jawo asara ga sojoji, 'yan sanda da 'yan banga wanda hakan yasa al'umma da dama suka gudu daga yankunan.
Saboda yawaitar ayyukan ta'addancin ne ya bukaci samar da jami'an tsaro na hadin gwiwa domin samar da tsaro a yankunan cikin gaggawa.
Yan bindiga sun kashe attajiri a Niger
A wani rahoton, kun ji cewa ana cikin jimami bayan mahara sun hallaka wani dan kasuwa a jihar Niger yayin da su ka afka masa a cikin shagonsa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin mai suna Alhaji Samiu Jimoh ya gamu da tsautsayin ne bayan maharani sun yi kokarin tafiya da shi amma ya ki.
Asali: Legit.ng