An Gurfanar da Mutumin da Ake Zargi da Safarar Makamai Ga ’Yan Bindiga a Kano
- Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da mutumin da take zargi da safarar makamai ga 'yan ta'adda a jihar Kano
- Mutumin dan asalin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara an kama shi ne a kauyen Gano da ke cikin Kano
- Bayan tattaunawa mai tsawo tsakanin lauyoyin wanda ake zargi da hukumar DSS, alkalin kotun ya yanke hukunci kan shari'ar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da wani mutum mai suna Jamilu Ibrahim da take zargi da mallakar makamai wanda ya sabawa dokar kasa.
Laifukan da ake zagin mutumin da su
Mutumin dan asalin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara ana zarginsa ne da mallakar harsashi guda 837, gurneti guda hudu da sauran mugayen makamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa an kama shi ne a ranar 19 ga watan Fabrairu a kauyen Gano da ke karamar hukumar Warawa ta jihar Kano.
Har ila yau ana zargin Jamilu Ibrahim da safarar makami ga 'yan bindiga da suke ayyukan ta'addanci.
Jawabin lauyoyi a gaban kotu
Amma da ake tuhumarsa da laifuffukan, bai amince da aikatasu ba, kuma lauyansa ya bukaci kotun ta bada belinsa.
Sai dai lauyar masu shigar da kara, Hassana Habib ta ce bai kamata a bada belin mutumin da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ba.
Lauyar gwamnati ta kara da cewa akwai yiwuwar zai gudu idan aka bada belinsa.
Hukuncin da kotu ta yanke
Alkalin kotun, mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, ya ki amincewa da bada belin tare da cewa zargin da ake yi wa mutumin suna da girma.
A karshe dai an tura shi gidan gyaran hali domin cigaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Mayu.
'Yan sanda sun kama 'yan bindiga a Sokoto
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kashe wani ɗan bindiga a yayin wani artabu da jami'anta suka yi da miyagu.
Kwamishinann ƴan sandan jihar ya tabbatar da cewa rundunar ta cafke mutum 15 da ake zargin ƴan bindiga a samamen da ta kai lokuta daban-daban a jihar.
Asali: Legit.ng