IPOB Ta Yi Barazanar Korar EEDC Daga Kudu Maso Gabas Saboda Rashin Wutar Lantarki

IPOB Ta Yi Barazanar Korar EEDC Daga Kudu Maso Gabas Saboda Rashin Wutar Lantarki

  • Masu fafutukar kafa kasar Biafra sun yi barazanar rufe kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu saboda rashin wutar lantarki
  • Kungiyar IPOB ta kuma zargi kamfanin EEDC da damfarar mutane ta hanyar cajarsu kudin wuta mai yawa alhalin ba sa samun wutar
  • Kungiyar ta yi kira ga kamfamim EEDC da ya samar da isasshiyar wutar lantarki ko kuma ya fice daga yankin Kudu maso Gabas

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Biyo bayan rashin wutar lantarki a yankin Kudu maso Gabas, masu fafutukar kafa kasar Biafra sun yi barazanar rufe kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu.

IPOB ta ba EEDC wa'adin gyara wutar lantarki a Kudu Maso Gabas
IPOB ta yi barazanar rufe ofishin EEDC kan matsalar wutar lantarki a Kudu Maso Gabas. Hoto: @therleez
Asali: Twitter

"EEDC na damfarar mutane" - IPOB

Kungiyar IPOB ta baiwa kamfanin EEDC wa’adin inganta wutar lantarki a yankin ko kuma ya fuskanci fushin kungiyar kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Kotun Kano ta dakatar da karbar sabon kudin wutar lantarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta yi kira ga shugaban kamfanin Enugu DisCo, Emeka Offor, da ma'aikatan kamfanin da su daina damfarar mutane.

Ta kara da cewa kamfanin na tilastawa mazauna yankin biyan “kudin wutar lantarki da aka kiyasta ba bisa ka’ida ba” wadanda suka kai dubunnan daruruwan Naira.

IPOB ta gargadi kamfanin EEDC

Kamar yadda wata sanarwa da sakataren yada labarai, Emma Powerful ya fitar a ranar Asabar; IPOB ta ce tana kira ga kamfanin EEDC da ya daidaita wutar lantarki a yankin.

"Idan suka ci gaba da kin ba da isasshiyar wutar lantarki a yankin Kudu maso Gabas, IPOB ba ta da wani zabi illa ta rufe ofisoshin EEDC.
“Idan wutar ta lalace, mutane ke hada kudi sayi taransifoma da keburan wutar lantarki. A haka kuma za su biya ma'aikatan EEDC su zo su hada masu wutar."

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin kawo hanyar da za ayi sallama da matsalar lantarki

- A cewar sanarwar.

IPOP za ta kori kamfanin EEDC

Jaridar The Punch ta rahoto kungiyar ta IPOB ta kuma yi zargin cewa EEDC ta tafi da wasu taransifomomi na wasu garuruwa domin gyarawa amma ta ki dawo da su.

Kungiyar ta yi kira ga EEDC da ya samar da isasshiyar wutar lantarki ko kuma ya fice daga yankin Kudu maso Gabas, inda ta yi gargadin cewa za ta kori EEDC idan ya gaza biyan bukatunsa.

Sabani ya barke a kungiyar IPOB

Gwamnatin Jamhuriyar Biafra ta 'yan gudun hijira (BRGIE), ta yi tir da kungiyar IPOB kan umarnin 'zama a gida' da ta bayar domin karrama jaruman Biafra da aka kashe a yakin basasar 1967-1970 a Najeriya.

Legit Hausa ta ruwaito Firayim Ministan BRGIE, Simon Ekpa ya ce ba za su yi zaman gida na kwana 1 kawai ba, dole a zauna dagaranar 29 zuwa 31 ga Mayu 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.