Kungiya Ta Maka Gwamnoni 36 da Minista Wike a Kotu Kan Cin Bashin N5.9tn da $4.6Bn
- SERAP ta maka gwamnonin Najeriya a kotu kan yadda suke cin bashin manyan kudade ba tare da yiwa ‘yan kasa bayani ba
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da taso ‘yan siyasar kasar nan a gaba kan yadda suke cin bashi ba tare da tunanin yadda za a biya ba
- Najeriya dai na ci gaba da fadawa yanayi na kunci bayan da komai ke tashi, haka nan ana ci gaba da cin bashi da sunan yiwa kasa aiki
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
FCT, Abuja - Kungiyar kare hakkin tattalin arziki ta SERAP ta shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Haka kuma a cikin karar ta ambaci gwamnonin jihohi 36 kan rashin ba da bahasi da wallafa yarjejeniyar lamunin Naira tiriliyan 5.9 da dala biliyan 4.6 da jihohinsu da babban birnin tarayya Abuja suka jajubo.
Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce kungiyar ta roki kotun da ta tilasta wa gwamnonin da Wike da su ba da bahasin kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ku yiwa ‘yan kasa bayani, SERAP ga gwamnoni
Hakazalika, ta bukaci su wallafa yarjejeniyar da aka kulla na karbo lamunin da kuma bayyana inda aka yi ayyukan da aka karbo kudin don yi, Channels Tv ta ruwaito.
A cewasr SERAP, ta shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/592/2024 ne a ranar Juma’a a madadin kumgiyar ta hannun lauyoyinta - Kolawole Oluwadare, Kehinde Oyewumi da Valentina Adegoke a babban birnin kasar.
Karar dai ta biyo bayan wata karar da SERAP ta shigar mai kunshe da mutane 37 da ake kara a ranar 31 ga Maris, 2024, bayan da gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya koka da tarin bashin da Nasir El-Rufai ya bar masa.
Babban abin da SERAP ke bukata
Bisa ga bukatar karar, SERAP na son kotu ta umarci tilastawa gwamnonin da Wike da su gayyaci EFCC da ICPC da ama sauran hukumomi masu hakki kan tattalin arzikin kasa da don bincika yadda aka kashe kudaden, rahoton jaridar Punch.
"Rashin sanin yadda aka kashe kudaden da gwamnonin da Wike suka ci bashi zai ci gaba da yin mummunan tasiri a kan muhimman bukatun 'yan kasa."
SERAP ta bukaci a bayyanawa al’umma yadda ake kashe kudaden kasar nan, musamman wadanda aka runtumo da sunan bashi don gujewa sace su ba gaira ba dalili.
SERAP ta maka gwamnatin Tinubu a kotu
A wani labarin kuma, SERAP bata bar gwamnatin tarayya ba, inda ta maka ta a kotu kan batun sanya linzami ga amfani da yanar gizo a Najeriya.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ke ci gaba da tsiro da abubuwan da za su ba gwamnati damar sanya ido kan komai.
Najeriya dai kasa ce da ke da adadi mai yawa na masu amfani da yanar gizo, sanya dokar babban barazana ce ga 'yan kasar.
Asali: Legit.ng