An Shiga Jimamin Rashin Daliba Aishat a Jami’ar Aliko Dangote Bayan Tsintar Gawarta a Daki
- Jami’ar Aliko Dangote ta fitar da jawabi kan gaskiyar abin da ya faru a mutuwar wata daliba ‘yar aji uku
- Dalibai sun bayyana yadda dalibar ta rasu a cikin dakinta da ke wajen makaranta bayan rubuta jarrabawa
- Ba sabon lamari bane samun mutuwar dalibai a ciki ko wajen jami’a ba, hakan ya sha aukuwa a wurare da dama
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Kano - Wani mummunan lamari ya afku a ranar Alhamis a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano, inda aka tsinci gawar wata daliba mai suna Aishat Yahaya Olabisi a wani gidan da take zaune a wajen jami’ar.
An tsinci gawar Aishat, wacce daliba ce ‘yar aji uku a fannin fasahar abinci da kimiyya bayan ta dawo dakinta daga makaranta.
An kuma ce, dalibar da ta rasu ta rubuta jarrabawarta ta farko a zangon farko na shekarar karatu ta jami’ar, The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane yanayi Aishat take kafin shigarta jarrabawa?
Daya daga cikin daliban da ta zanta da jaridar Punch a ranar Asabar ta dora laifin rasuwar ta fuji’a da matsin jarrabawa.
A cewarta:
“Lafiyarta kalau lafin ta tafi rubuta jarrabawarta ta farko a zangon farko da ake gudanarwa.”
Sai dai, bayan jita-jitar da aka yada cewa dalibar ta rasu ne a dakin karatun da ke cikin jami’ar, tuni mahukunta a jami’ar suka fayyace komai.
Bayanin da jami’ar Aliko Dangote ta fitar
A wata sanarwar da shugaban kula da harkokin dalibai na jami’ar, farfesa Abdulkadir Dambazau ya fitar a ranar 3 ga watan Mayu, ya ce ba a cikin jami’ar ta rasu ba.
Ya kuma bayyana matakan da jami’ar ta dauka na binciken inda dalibar take bayan rashin ganinta, inda daga baya aka gano ta mutu a dakinta.
Ya zuwa yanzu, an dauki gawar Aishat zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke birnin Kano don bincika gawar.
An tsince gawar daliba a UNIPORT
A wani labarin kuma, kun ji yadda aka tsince gawar wata dalibar jami’a a jihar Rivers a cikin dakinta.
Wannan lamari ya tada hankali, inda tuni aka fara binciken sanadiyyar mutuwarta tare da daukar mataki.
A cewar majiya, dalibar ta mutu a dakinta da ke wajen makaranta bayan ta dawo daga karatu.
Asali: Legit.ng