'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malaman Addini Suna Kan Hanyar Zuwa Yin Wa'azi

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Malaman Addini Suna Kan Hanyar Zuwa Yin Wa'azi

  • Ƴan bindiga sun yi awon gaba da Archbishop Uka Uka Osim na cocin Brotherhood of the Cross and Star a jihar Abia
  • Tsagerun sun yi awon gaba malamin addinin ne tare da matarsa da ɗansa da wasu fastoci uku lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa birnin Awka na jihar Anambra
  • Shugaban cocin a jihar Abia ya bayyana cewa har yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi kowa ba kwanaki huɗu bayan sun yi garkuwa da mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Archbishop Uka Uka Osim na cocin Brotherhood of the Cross and Star, matarsa, Anne Osim da ɗansa, Roland Uka Osim.

An dai sace su ne tare da wasu limaman cocin Brotherhood of the Cross and Star su uku a jihar Abia a ranar 1 ga watan Mayun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Rundunar sojoji ta kammala bincike kan harin bam da ya hallaka masu Maulidi

'Yan bindiga sun sace Fastoci a Abia
'Yan bindiga sun sace Fastoci shida a jihar Abia Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya auku

Suna tafiya ne zuwa Awka, babban birnin jihar Anambra, domin gudanar da aikin wa’azi a lokacin da ƴan bindigan suka sace su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran limaman cocin guda uku da aka yi garkuwa da su sun haɗa da Azuka Ochu, Moses Okafor da Anderson Akwazie.

Shugaban cocin a jihar Abia, Bishop Denis Onuoha, shi ne ya tabbatar da yin garkuwar da aka yi da su, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Ya ce har yanzu ƴan bindigan ba su tuntuɓi kowa ba kwanaki huɗu bayan aukuwar lamarin.

A kalamansa:

"Mun damu matuƙa amma muna da tabbacin cewa ubangiji da suke bautawa kuma suke yi masa aiki da zuciya ɗaya zai kai musu ɗauki."

An yi kira ga jami'an tsaro

Yayin da ya yi kira ga jami’an tsaro da su zage damtse domin kuɓutar da limaman, ya ce sun zurfafa yin addu’o’in domin ganin sun kuɓuta ba tare da wani rauni ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban PDP tare da sace mawaki a Delta

Hukumomin ƴan sanda a jihohin Anambra da Abia har yanzu ba su mayar da martani kan lamarin ba.

Ƴan bindiga sun kai hari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi wa Askawaran Zamfara kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun hallaka jami'ai uku a yayin harin tare da yin awon gaba da makamai da baburan jami'an tsaron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng