An Shiga Fargaba Bayan 'Yan Bindiga Sun Shiga Garuruwan Katsina, An Hallaka Mutane 24

An Shiga Fargaba Bayan 'Yan Bindiga Sun Shiga Garuruwan Katsina, An Hallaka Mutane 24

  • An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun yi ajalin mutane 24 a jihar Katsina wadanda mafi yawanci 'yan banga ne
  • Maharan sun kai farmaki a unguwar Sarkin Noma da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar a daren ranar Alhamis
  • Shugaban karamar hukumar, Faruq Dalhatu ya tabbatar da kai harin inda ya ce an yi sallar jana'izar mutanen da safiyar ranar Juma'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun kai mummunan hari a jihar Katsina inda suka hallaka mutane 24.

Harin ya yi sanadin jikkata mutane da dama a Unguwar Sarkin Noma da ke karamar hukumar Sabuwa a jihar.

'Yan bindiga sun kuma hallaka mutane 24 a Katsina
'Yan bindiga sun kai farmaki a Katsina tare da hallaka mutane 24. Hoto: Dikko Umar Radda.
Asali: Twitter

Su waye aka fi hallakawa a Katsina?

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna, sun hallaka 'yan banga tare da sace sarakuna 2

Mafi yawan wadanda aka hallaka 'yan banga ne da suka zo domin tunkarar 'yan bindigan a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Channels TV ta tattaro cewa maharan sun farmaki 'yan bangan ne yayin da suke shan matsi daga hare-haren sojoji.

Majiyar tsaro ta tabbatar cewa maharan sun kai farmakin ne a ranar Alhamis 2 ga watan Mayu da misalin karfe 9:00 na dare, cewar Radio Nigeria.

Daga cikin wuraren da harin ya shafa akwai Unguwar Sarkin Noma da Gangara da Tafi da kuma Kore.

Maganar shugaban karamar hukumar

Shugaban karamar hukumar Sabuwa, Dalhatu Faruq ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce abin takaici ne.

Dalhatu ya ce tuni aka binne mutane 23 a safiyar ranar Juma'a 3 ga watan Mayu kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Ya ce sauran mutum ɗaya da ya rage wanda ke asibiti shi ma an tabbatar da mutuwarsa daga bisani.

Kara karanta wannan

Fadan daba: fusatattun matasa sun cinnawa kasuwa wuta a Lagos

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Abubakar Sadiq bai yi martani kan lamarin ba.

Yan bindiga sun kai hari a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun sake kai hari a jihar Kaduna inda suka hallaka 'yan banga takwas.

Yayin harin da maharan suka kai, sun kuma yi garkuwa da wasu sarakunan gargajiya biyu a yankin da ke karamar hukumar Birnin Gwari.

Wannan na zuwa ne bayan wani mummunan hari da 'yan bindigan suka kai tare da hallaka wani Dagaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.