"Buhari Ya Daura Shugaban APC Duk da Zargin Cin N15bn", Tsohon Minista Ya Tona Asiri
- Tsohon Minista a Najeriya, Edwin Clark ya koka kan yadda masu mukamai ke handame makudan kudi a kasar
- Clark ya ce tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya daura tsohon shugaban APC, Abdullahi Adamu duk da zargin badakala
- Dattijon ya ce akwai 'yan APC da dama da ake zarginsu da cin hanci amma yanzu suna yawo ba tare da an tuhume su ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Neja Delta (PANDEF), Edwin Clark ya zargi tsohon shugaban kasa, Muhammad Buhari da marawa cin hanci baya.
Clark ya ce Buhari ya kakabawa APC Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam'iyyar duk da zargin badakalar kudi.
Wane zargi EFCC ke yi kan Adamu?
Dattijon ya ce hukumar EFCC na zargin Abdullahi Adamu da badakalar kudi wanda bai kamata a ba shi kujera mai girman haka ba, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon ministan ya bayyana haka yayin hira da 'yan jaridu inda ya ce tsoffin gwamnoni da dama ana zarginsu da cin hanci a Najeriya.
Ya koka kan yadda wasu 'yan siyasa da suka tafka badakalar kudi ke samun 'yanci a Najeriya ba tare da ɗaukar mataki kansu ba, cewar Daily Post.
Yadda Buhari ya daura shugaban APC
"A 2007 fiye da tsoffin gwamnoni da ministoci 15 aka gurfanar da su a gaban kotu lokacin da Nuhu Ribadu ke jagorantar hukumar EFCC."
"Daga baya bamu sake jin komai ba, wasu an tantance su domin tsayawa takarar sanata a jihohinsu."
"Misali tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu an gurfanar da shi kan badakalar N15bn lokacin da ya ke mulkin jihar."
"Bayan haka, ya tsaya takarar sanata kuma ba a sake magana ba, daga bisani Buhari ya kakaba shi a matsayin shugaban jami'yyar APC."
- Edwin Clark
Clark ya ce a yanzu akwai 'yan APC da dama wadanda suka ci dukiyar jama'a dumu-dumu kuma babu wanda ya ke magana.
Ya ce yanzu da yawansu an wanke su sun dawo suma suna magana kan cin hanci da rashawa.
Sai dai a ka'ida, ba shugaban kasa ne yake da alhakin daura shugaban jam'iyya ba.
"Ba zamu zargi Buhari ba" - Shettima
A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana irin tsare-tsaren da Shugaba Bola Tinubu ya kawo.
Kashim ya ce ba za su ci gaba da zargin gwamnatin Muhammadur Buhari ba illa neman hanyar kawo mafita.
Asali: Legit.ng