Gwamna Ya Naɗa Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya a Shirgegen Mukami a Jiharsa

Gwamna Ya Naɗa Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya a Shirgegen Mukami a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya nada tsohon hafsan sojojin Najeriya mukami a gwamnatinsa domin inganta tsaro
  • Gwamnan ya nada Laftanar-janar Azubuike Ihejirika mai ritaya a matsayin shugaban kwamitin tsaro a jihar baki daya
  • Sakataren yada labaran gwamnan, Kazie Uko shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 3 ga watan Mayu inda ya ce za su fara aiki nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya kaddamar da kwamitin tsaro domin tabbatar da inganta zaman lafiya.

Mai girma Gwamnan ya kuma yi wasu muhimman nade-nade da za su taimaka wurin tabbatar da samun tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

ICPC: Kotu ta umarci cafke sojan da ya nemi takaran Gwamna da wasu mutane 2

Gwamna ya nada tsohon hafsan sojoji mukami
Gwamna Alex Otti ya nada tosohn hafsan sojoji, Laftanar-janar Azubuike Ihejirika mukami a jihar Abia. Hoto: Alex Otti.
Asali: Twitter

Abia: Wanene gwamna Otti ya ba mukami?

Alex Otti ya nada tsohon hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Azubuike Ihejirika mai ritaya a matsayin shugaban kwamitin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Kazie Uko ya fitar a shafin Facebook a yau Juma'a 3 ga watan Mayu.

Yayin da aka naɗa tsohon mataimakin sifetan 'yan sanda, Uche Ivy Okoronkwo a matsayina mataimakin shugaban kwamitin.

Sauran wadanda aka ba mukami a Abia

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Ray Nkemdirim da Manjo-janar Abel Obi Umahi mai ritaya da AVM Emmanuel Chukwu mai ritaya.

Sakataren yada labaran gwamnan ya ce dukkan nade-naden da mai gidansa ya yi za su fara aiki nan take ba tare da bata lokaci ba.

Sai kuma wadanda suke kwamitin tallafin tsaro sun hada da Cif Stanley Obiamarije a matsayin shugaba, sai Owelle Greg Okafor.

Kara karanta wannan

Sabon mafi karancin albashi: Gwamnoni sun yi wa ma'aikata kyakkyawan albishir

Sauran sun hada da Ngozi Ekeoma da Johnson Chukwu da Josephine Nweze da Nkechi Obi da Bank-Anthony Okoroafor.

Kotu ta umarci kama tsohon hafsan sojoji

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta umarci kama tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya, Usman Jibrin.

Kotun ta ba da wannan umarni ne kan zargin badakalar N1.5bn da ake yi wa tsohon shugaban sojojin tare da wasu mutane biyu.

Hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ita ta gurfanar da Usman da mutanen biyu a gaban kotu kan zargin badakala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.