Yadda ’Yan Sandan Kano Suka Yi Wawason ’Yan Daba Sama da 3000 a Shekara 1

Yadda ’Yan Sandan Kano Suka Yi Wawason ’Yan Daba Sama da 3000 a Shekara 1

  • Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Usaini Gumel ya tabbatar da nasarar rundunarsa wurin kama masu laifi 3,000
  • Yayi bayanin ne yayin da yake hira da manema labarai a kan nasorin da rundunar ta samu a jihar cikin shekara guda
  • Ya kuma jaddada cewa rundunar 'yan sanda za ta cigaba da farautar 'yan ta'adda a fadin jihar har sai ta ga bayansu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta yi nasarar cafkewa tare da gurfanar da masu laifi 3,000 a cikin shekara guda.

Kanao CP
Rundunar 'yan sanda ta samu nasara kan yaki da 'yan ta'adda a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ne ya bayyana haka wa 'yan jarida.

Kara karanta wannan

An yi abin kunya bayan kama jarumin fina finai da zargin sace budurwa mai shekaru 14

Rahoton jaridar Tribune Online ta tabbatar da cewa kwamishinan ya bayyana adadin ne yayin da yake lissafa nasarorin da rundunar ta samu cikin shekara guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya kara nuni da cewa yawanci wadanda aka kama din masu aikata manya-manyan laifuka ne.

Nau'ukan masu laifin da aka kama

Daga cikin nau'ikan masu laifin da aka kama sun hada da masu garkuwa da mutane, 'yan bindiga, masu fashi da makami.

Cikin wadanda aka kama har da masu safarar mutane zuwa kasashen ketare, dilolin kwaya da 'yan daba.

CP Gumel ya kara da cewa sun kara fadada harkar gyaran hali yayin da suka bada horo na musamman ga 'yan daba 623 da suka tuba.

Ya kara da cewa 'yan daban da suka tuban an koya musu sana'o'i daban-daban a karkarshin tallafin da gwmantin jihar ta bayar.

Kara karanta wannan

Fadan daba: fusatattun matasa sun cinnawa kasuwa wuta a Lagos

Kawar da 'yan daba a Dutsen Dala

Kwamishinan ya bayyana irin kokarin da rundunarsa take wurin kawar da barna da 'yan daba a Dutsen Dala, cewar jaridar Premium Times.

Ya ce rundunar ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen tsaftace Dutsen domin ya kunshi yanki na musamman a tarihin jihar Kano.

Kawar da mabarnata a dazukan Kano

Ya kara tabbatar da cewa akwai wasu bata garin masu barna a yankin jejin Falgore da Danshoshiya.

Suna aikata laifukan garkuwa da mutane, sayen kayan sata da harkokin kwaya da sauransu a cikin dazukan.

A karshe kwamishinan ya ce ya lashi takobin tabbatar da zaman lafiya da doka da oda a fadin jihar.

'Yan daba sun yi yunkurin kai hari Kano

A wani rahoton, kun ji cewa wasu ƴan daba sun yi yunkurin kawo hargitsi a bikin rantsar da sabbin kwamishinoni ciki har da ɗan Kwankwaso.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun yi nasarar cafke su ba tare da sun cimma burinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng