Tsohon Gwamnan Kwara Ya Halarci Kotu Yayin da EFCC Ta Gurfanar da Kwamishina Kan N1.22bn

Tsohon Gwamnan Kwara Ya Halarci Kotu Yayin da EFCC Ta Gurfanar da Kwamishina Kan N1.22bn

  • Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon kwamishinan kuɗi na jihar Kwara a gaban kotu
  • Hukumar EFCC na tuhumar Ademola Banu da karkatar da N1.22bn a lokacin da yake riƙe da wannan muƙamin a jihar
  • An dai gurfanar da shi ne tare da tsohon gwamnan jihar, Abdulfatah Ahmed bisa zargin haɗa baki wajen salwantar da kuɗaɗen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) a ranar Litinin, 30 ga watan Afrilu, 2024, ta gurfanar da Ademola Banu, a gaban kotu.

Ademola Banu ya taɓa rike muƙamin kwamishinan kuɗi a jihar Kwara, wacce ke a yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu vs El-Rufai: Jigon APC ya yi hasashen yadda 'yan Najeriya za su yi zaben 2027

Abdulfatah Ahmad ya halarci kotu
EFCC ta gurfanar da tsohon kwamishinan kwara kan badakalar N1.22bn Hoto: Alhaji Abdulfatah Ahmed, Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

An gurfanar da Ademola Banu a gaban babbar kotun tarayya dake Ilorin bisa zargin karkatar da kuɗaɗen jihar kimanin Naira biliyan 1.22, cewar sanarwar da hukumar ta fitar a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zargi EFCC ke yi masa?

Daga cikin zarge-zargen, EFCC ta ce Ademola Banu ya haɗa baki wajen karkatar da Naira biliyan 1.22 a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Abdulfatah Ahmed.

A yayin zaman kotu na farko, Ademola bai samu halarta ba, wanda hakan ya sanya alƙalin kotun ya ba da umurnin a kamo shi.

A yayin ci gaba da zaman kotun a ranar Litinin, 30 ga watan Afrilu, waɗanda ake ƙara, Abdulfatah Ahmed da Ademola Banu sun halarci zaman kotun.

Ademola Banu ya musanta aikata laifin bayan an karanto tuhume-tuhumen da ake masa a gaban kotun.

Daga nan sai lauyansa Gboyega Oyewole, SAN, ya gabatar da bukatar a bayar da belin wanda yake karewa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban PDP tare da sace mawaki a Delta

Kotu ta ba da beli

Gboyega Oyewole, SAN ya roƙi kotun da ta amince da buƙatar ba da belin inda ya kawo dalilai na rashin lafiyar wanda yake karewa.

Mai shari’a Evelyn Anyadike ta amince da buƙatar, inda ta bayar da belinsa a kan kuɗi N20m tare da kawo mutane biyu da za su tsaya masa, waɗanda suka mallaki kadarori.

Dole ne waɗanda za su tsaya masa su ajiye hotunan fasfo guda uku a wurin magatakardan kotun.

Sannan dole ne kuma su gabatar da shaidar biyan kuɗin wutar lantarki na watanni uku da suka gabata.

An ɗage shari'ar zuwa ranakun 25 zuwa 26 na watan Yuni domin ci gaba da sauraronta.

EFCC ta titsiye tsohon gwamna Abdulfatah

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon ƙasa, (EFCC), ta tsare tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.

EFCC ta titsiye tsohon gwamnan da tambayoyi kan yadda aka kashe wasu maƙudan biiyoyin Naira lokacin da yake mulkin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng