Dukiyar Marayu: Kotu Ta Daure Dattijon da Ya Cinye Gidaje da Motocin N12m

Dukiyar Marayu: Kotu Ta Daure Dattijon da Ya Cinye Gidaje da Motocin N12m

  • Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin shekara daya a gidan gyaran hali sakamakon cin dukiyar marayu a jihar Borno
  • Hukuma mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ne ta gurfanar da mutumin a gaban kotu cikin shekarar da ta wuce
  • Legit ta tattauna da wani malamin addinin Musulunci domin jin yadda hukuncin cin dukiyar marayu yake a mahangar Islama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Babbar kotun jihar Borno da ke birnin Maiduguri ta tura wani mutum mai suna Isiyaku Ibrahim gidan gyaran hali bisa cin dukiyar marayu.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu bayan samun mutumin da laifi dumu-dumu.

Kara karanta wannan

Wasu 'yan jam'iyyar APC sun yi kira ga EFCC kan cigaba da binciken ministan Tinubu

Ishaku
Alkali ya yankewa wani mutum zaman gidan gyran hali saboda cin dukiyar marayu. Hoto: Economic and Financial Crime Commission
Asali: Facebook

A bayanan da hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta wallafa a shafinta na Facebook ya nuna cewa an fara zargin mutumin ne tun shekarar da ta wuce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gurfanar da shi ne bisa zargin lakume dukiya da kadarorin da suka kai Naira miliyan 12 na marayu bisa son zuciya.

Dukiyar marayun da mutumin ya cinye

Ana zargi mutumin da cinye gidaje guda uku, filaye da aka zagaye guda biyu, gidan burodi guda biyu, filaye da ba a zagaye ba guda biyu, mota tanki guda biyu da babban janareta guda daya, wanda jimillar kudinsu ya kai Naira miliyan 12.

Hukuncin da kotu ta yi

A farko mutumin bai amince da laifinsa ba sai da aka gabatar da shaidu shida tare da takardun da suka tabbatar da lamarin.

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin kawo hanyar da za ayi sallama da matsalar lantarki

Bayan tabbatar da laifin, mai Shari'a Fadawu na kotun ya yanke masa hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekara guda ko kuma biyan taran N100,000.

Fadakarwa kan cin dukiyar marayu

Wani malamin addini, Muhammad Abubakar, ya ja hankalin al'umma kan cin dukiyar marayu ba ta hanyar shari'a ba.

Ya bayyana cewa cin dukiyar haramun ne kuma zalunci ne da Allah zai iya kama mutum tun a gidan duniya.

A cewar malamin, ya kamata mutane su rika hangen nesa da zurfafa tunani kan cewa suma za su iya mutuwa su bar marayu.

EFCC ta gano kudin makamai

A wani rahoton kun ji cewa hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana gano wasu daga kudin makaman da su ka yi batan dabo a kasar nan.

EFCC ta bayyanawa wata babbar kotu a Abuja yadda ta gano sama da Naira biliyan hudu a asusun Sagir Bafarawa, ɗan tsohon gwamnan jihar Sokoto.

Shaidar EFCC a kotun, Abdullahi ya ce sun binciki kamfanoni 78 da ake zargi da cin kudin makaman yakar ta'addanci a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng