'Yan Bindiga Sun Kai Ƙazamin Hari a Wurin Zaman Makoki, Sun Kashe Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Ƙazamin Hari a Wurin Zaman Makoki, Sun Kashe Bayin Allah

  • Ƴan bindiga sun kashe mutum huɗu yayin da suka kai farmaki wurin zaman makoki a jihar Enugu ranar Lahadi
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan, wadanda ake zargin fulani makiyaya ne sun sun kai harin ne ba zato ba tsammani
  • Har yanzun rundunar ƴan sanda ba ta ce komai ba kan lamarin wanda ya bar mutane cikin jimami da alhini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Wasu miyagun ƴan bindiga da ake zargin akiyaya ne sun kashe mutum huɗu a Ugwuijoro da ke kauyen Nimbo, ƙaramar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu.

An tattaro cewa maharan sun kai wannan farmaki ne a yammacin ranar Lahadi kuma mutane da dama sun samu raunuka.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa matafiya wuta, sun tafka ɓarna a titin Abuja-Kaduna

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutum 3 a Enugu Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Majiyoyi daga ƙauyen sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kai hari kan masu zaman makoki da manoma, lamarin da ya ƙara jefa mutane cikin alhini da jimami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin waɗanda aka kashe a harin sun haɗa da Okeh Simon Ugwu Oruku, Okeh Chukwuebuka, Julius Ogbonna Odiegwu da kuma Gabriel Ugwor Ezea.

Yadda aka kai hari wajen zaman makoki

Wani faifan bidiyo da jaridar The Nation ta gani ya nuna yadda mutanen ƙauyen suka tarwatse.

Wani mutumi da aka ji muryarsa a bidiyon ya bayyana cewa maharan sun mamayi mutanen ƙauyen ba zato ba tsammani, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Ana iya ganin tebura da kujeru a watse a cikin harabar gidan inda masu zaman makokin suka taru tare da gawarwakin waɗanda aka kashe kwance cikin jini.l, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

An kama mutum 2 yayin da wani gini mai bene ya kashe mutane a jihar Kano

Abin da ya faru a 2016

Miyagun ƴan bindiga sun taɓa kai mummunan farmaki kauyen Nimbo tun a shekarar 2016, inda mutane masu yawa suka rasa rayukansu.

Wannan lamari dai ya ja hankalin mutane a lungu da sako na ƙasar nan a wancan lokaci.

Har yanzu da muke haɗa maku wannan rahoton rundunar ƴan sanda reshen jihar Enugu ba ta fitar da wata sanarwa ko amsa sakonnin da aka tura mata kan lamarin ba.

Nasarorin sojoji a mako ɗaya

A wani rahoton na daban, dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 216 kuma sun kama wasu miyagu 332 a samame daban-daban a faɗin ƙasar nan cikin mako ɗaya.

Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262