Ana Tsaka da Dambarwar Yahaya Bello, Hukumar EFCC Ta Yi Garambawul a Mukamai
- Yayin da ya ke ta kokarin kawo karshen cin hanci da rashawa, shugaban EFCC ya yi garambawul a hukumar da sabbin nade-nade
- Ola Olukoyede ya nada sabon shugaban ma'aikatansa da kuma wasu sabbin darektocin yankuna 14 a fadin ƙasar
- Hakan ya zo a dai-dai lokacin da hukumar ke cikin dambarwa da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello kan badakalar N84bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya yi sabbin nade-nade a hukumar.
Olukoyede ya amince da sabbin darektoci 14 a yankuna domin tabbatar da inganta ayyukan hukumar da kuma sauke nauyin da aka daura musu.
Waye aka nada shugaban ma'aikatan EFCC?
Har ila yau, shugaban hukumar ya nada Michael Nzekwe a matsayin shugaban ma'aikatansa, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nzekwe ya kasance kwararren lauya wanda kuma shi ne tsohon kwamandan yanki na hukumar da ke birnin Ilorin a jihar Kwara.
Sakataren yada labaran hukumar, Dele Oyewale shi ya tabbatar da haka a yau Asabar 27 ga watan Afrilu, cewar Punch
Olukoyede ya daga darajar ofisoshin yankin inda ya nada darekta a kowane bangare domin tabbatar yin aiki tukuru a kokarin yaki da cin bana.
An kuma kirkiri wani sabon ofishi a karkashin shugaban hukumar wanda tsohon kwamandan yanki a Makurdi, Friday Ebelo zai jagoranta.
Musabbabin yin sabbin nade-nade a EFCC
"Nzekwe kwararren mai gudanarwa ne wanda ya halarci kwasa-kwasai da dama a gida da kuma kasashen ketare."
"Dukkan nade-naden za su fara aiki ne nan take ba tare da bata lokaci ba."
"Olukoyede ya ce wannan garambawul din an yi ne saboda inganta ayyukan hukumar a kokarin dakile matsalar cin hanci a Najeriya."
- Dele Oyewale
Kotu ta bada sabon umarni ga shugaban EFCC
A wani labarin, kun ji cewa wata babbar kotu a jihar Kogi ta umarci shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya gurfana a gabanta.
Kotu ta ba shugaban hukumar kwanaki inda ta ce dole ya hallara kan zargin saɓa umarninta a binciken tsohon gwamna jihar, Yahaya Bello.
Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ke tuhumar tsohon gwamnan kan badakalar N84bn lokacin da ya ke mulkin jihar.
Asali: Legit.ng