Yahaya Bello Ya Yi Martani Kan Zargin Biyan Kudin Makarantar 'Ya'yansa Daga Asusun Kogi
- Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya musanta zargin cewa ya ɗebi kuɗaɗen jihar Kogi ya biya kuɗin makarantar ƴaƴansa
- Yahaya Bello ya musanta zargin na hukumar EFCC cewa ya cire kuɗaɗen ne daga asusun jihar yana dab da barin kujerar mulki
- A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, ya bayyana cewa an biya kuɗaɗen ne tun a shekarar 2021
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ƙaryata iƙirarin cewa ya cire kuɗi daga asusun gwamnatin jihar domin biyan kuɗin makarantar ƴaƴansa a makarantar American International School da ke Abuja, kafin ya bar mulki.
Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa Ta’annati (EFCC), Olanipekun Olukoyede, ya yi wannan zargin yayin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, 2024.
Da yake mayar da martani kan zargin, Bello ya ce maganar da EFCC ta yi kan biyan kuɗin makarantar ƴaƴansa ba gaskiya a ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Yahaya Bello kan harkokin yaɗa labarai, Ohiare Michael ya sanya wa hannu.
Wane martani Yahaya Bello ya yi?
Yahaya Bello ya ce ƴaƴansa sun yi karatu a makarantar tun kafin ya zama gwamna ba tare da ya gaza biya ba, cewar rahoton jaridar The Punch.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Mai girma, Alhaji Yahaya Bello bai biya Dala 720,000 ba kamar yadda shugaban EFCC ya yi zargi ko kuma Dala 840,000 da ake yaɗawa a yanar gizo."
"Ba a biya ƙuɗin ba a lokacin da mai girma tsohon gwamna zai bar ofis kamar yadda Mista Olanipekun Olukoyede ya yi iƙirari, amma an biya su ne a shekarar 2021."
“Alhaji Yahaya Bello bai biya kuɗin makarantar ƴaƴansa ba daga asusun gwamnatin jihar Kogi."
Ya yi bayanin cewa wani daga cikin ƴan uwan Yahaya Bello ya ƙalubalanci hukumar EFCC lokacin da ta yi ƙoƙarin ƙwato kuɗaɗen da aka biya a makarantar.
A cewar sanarwar, takardun shaidar biyan kuɗaɗen da EFCC ta wallafa a yanar gizo, lauyoyin Yahaya Bello ne suka fitar da su domin nuna cewa ba shi da wani abun ɓoyewa.
Yahaya Bello ya ƙalubalanci EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa ofishin yaɗa labarai na tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya musanta cewa hukumar EFCC ta taɓa gayyatarsa.
Shugaban ofishin yaɗa labaran, Ohiare Michael, ya ce EFCC ba ta taɓa aika wa Yahaya Bello wani goron gayyata ba amma ta ci gaba da bayyana cewa ana nemansa.
Asali: Legit.ng