Hukumar EFCC ta Musanta yi wa Tsohon Gwamnan APC Bita da Kulli a Shari'ar N80bn

Hukumar EFCC ta Musanta yi wa Tsohon Gwamnan APC Bita da Kulli a Shari'ar N80bn

  • Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukayide ya musanta cewa ya na yiwa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello bita-da-kulli
  • Ola Olukayide ya bayyana cewa shi ma gadar fayil din binciken ya yi, wanda tuni ya gano akwai matsaloli kuma dole ayi bincike
  • Ya bayyana cewa idan ba a binciki badakalar da ake zargin Yahaya Bello da yi ba, ba za a iya bincikar kowa ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukayide ya musanta zargin cewa shi ne ya fara bincikar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

A tattaunawarsa da manema labarai a ranar Talata a Abuja, shugaban hukumar ya ce shi ma gadar binciken ya yi daga tsohon shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya dauki $720,000 ya biya kudin makarantar yaronshi a waje, Shugaban EFCC

Hukumar EFCC ta ce ba ta bibiyar gwamnan Kogi da muguwar manufa
Shugaban EFCC, Ola Olukayede ya bayyana cewar gadar fayil din binciken Yahaya Bello ya yi Hoto: Alhaji Yahaya Bello/Ola Olukayede
Asali: Facebook

Shugaban ya ce ba shi da dalilin yi wa Yahaya Bello bita da kulli, kamar yadda Premium Times ta wallafa labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“ Ba ni na fara binciken ba; gadar fayil din binciken na yi. Na kuma nemi a kawo min shi, na ce akwai matsala a nan,”

- Ola Olukayede

"Mun samu nasarori" Inji EFCC

Ola Olukayode ya kara da cewa ya na kishin ganin an samu ci gaba a Najeriya, wanda a cikin watanni shidan fara aikinsa, hukumar ta kwato Naira biliyan 120 daga hannun ‘yan damfara.

Ya musanta cewa su na aiki da son zuciya tun bayan da ya kama aiki a shekarar 2023, inda ya ce idan ba su bibiyi shari’ar Yahaya Bello ba, ba za su iya bincikar kowa ba, Leadership News ta ruwaito.

Shugaban EFCC ya kuma ce sun samu nasara a kotu kan wasu mutane 1600 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, wadanda tuni aka daure su.

Kara karanta wannan

Badakalar $720, 000: Yadda muka yi da tsohon gwamna Yahaya Bello Inji Shugaban EFCC

Yahaya Bello na son gurfana gaban kotu

A baya kun ji tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da yanzu haka ke fuskantar zargin sama da fadi da kudin al’ummarsa ya bayyana cewa ya na son a gurfanar da shi gaban kotu.

Sai dai lauyansa, Adeola Adedipa SAN ya bayyana fargabar umarnin da kotu ta bayar na a cafke shi, inda ya roki kotun ta soke umarnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.