Yadda Hukumar EFCC Ta Samu Nasarar Kwato N120bn a Cikin Watanni 6

Yadda Hukumar EFCC Ta Samu Nasarar Kwato N120bn a Cikin Watanni 6

  • Ola Olukoyede wanda ya ke shugabantar hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ya faɗi wasu nasarorin da ya samu
  • Olukoyede ya bayyana cewa a cikin watanni shida da ya shafe yana jagorantar hukumar, an samu nasarar ƙwato Naira biliyan 120 daga hannun ƴan damfara
  • Ya yi nuni da cewa Najeriya tana buƙatar hukumsr EFCC ta tsira domin ci gaba da farautar masu aikata laifukan da suka shafi satar kuɗaɗe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan nasarorin da hukumar ta samu tun bayan da ya fara jagorantarta.

Olukoyede a ranar Talata ya bayyana cewa hukumar ta ƙwato Naira biliyan 120 daga hannun ƴan damfara a Najeriya cikin watanni shida da hawansa mulki.

Kara karanta wannan

Badakalar N18bn: EFCC ta sake shigar da sabuwar kara kan Godwin Emefiele

EFCC ta kwato N120bn
EFCC ta kwato N120bn cikin watanni 6 Hoto: @OfficialEFCC
Asali: UGC

TABLE OF CONTENTS

Ya bayyana hakan ne a Abuja a wani taron manema labarai a hedikwatar hukumar ta EFCC, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa hukumar EFCC ta ƙwato zuwa yau?

Olukoyede ya jaddada cewa Najeriya na bukatar EFCC domin tsira yayin da hukumar ke ci gaba da ƙwato kuɗaɗen sata daga hannun mutane kusan kullum.

"Muna buƙatar EFCC, muna buƙatar wannan hukuma domin mu tsira, mun share hawayen mutane da dama da aka cuta, mutane masu ɗumbin yawa da aka zalunta, kullum muna ci gaba da ƙwato kuɗaɗe a hannun mutane."
"A cikin watanni shida da na yi, mun ƙwato sama da Naira biliyan 120 kuma mun sanya an yanke hukunci sama da 1,600."

- Ola Olukoyede

Batun binciken Yahaya Bello a EFCC

Shugaban na hukumar EFCC ya kuma zargi tsohon gwamnan jihar Kogi da cire kuɗi daga asusun gwamnatin jihar Kogi domin biyan kuɗin makarantar yaransa.

Kara karanta wannan

Daga karshe Ganduje ya bayyana wadanda suka kitsa dakatar da shi daga jam'iyyar APC

Olukoyede ya zargin Yahaya Bello da cirar Dala dubu 720 domin biyan kuɗin makarantar ƴaƴansa, inda ya sha alwashin cewa zai ajiye aiki idan bai kammala binciken tsohon gwamnan ba, cewar rahoton tashar Channels tv.

EFCC ta shigar da ƙara kan Emefiele

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC ta sake shigar da sabuwar ƙara kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

A cikin ƙarar da hukumar yaƙi da cin hancin ta shigar, ta zargi Emefiele ta zargi amfani da sanya hannu kan buga N684m a kan kuɗi har N18.9bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng