Kwararren Mai Kerawa Boko Haram Bama Bamai Ya Mika Wuya a Borno
- Shahararren mai kera wa 'yan kungiyar Boko Haram bama-bamai ya mika wuya ga jami'an tsaro a jihar Borno
- Kakakin rundunar hadin kai mai yaki da ta'addanci a jihar Borno, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ne ya bada sanarwar
- Ya kuma yi kira ga sauran 'yan ta'addan da ke boye cikin dazuka da su fito su mika wuya ga jami'an tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kwararren mai kerawa kungiyar ta'addanci ta Boko Haram bama-bamai tare da wani dan kungiyar guda daya sun mika wuya ga jami'an tsaro a jihar Borno.
Mutanen sun mika wuya ne ga jami'an sashen na uku na rundunar haɗin guiwa mai yaki da ta'addanci da ke Munguno a jihar Borno.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa sun mika wuyan ne ranar Lahadi, 21 ga watan Afrilu bayan an umurcesu da su kai hari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan ta'addan da suka mika wuya
Sanarwar da kakakin rundunar, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi, ya bayar ta nuna cewa mai hada bama-baman ya ce sunansa Abubakar Muhammad (Garba) kuma shekarunsa 19 ne.
Daya dan ta'addan da suka mika wuya tare kuwa sunansa Bana Modu mai shekaru 13 da haihuwa, a cewar jaridar Premium Times
Kakakin ya kara da cewa lokacin da ake bincikensu sun tabbatar da cewa an umarce su ne da su dasa bama-bamai a titunan garin Baga da ke karamar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Amma a cewarsu, sai suka mika wuya ga jami'an tsaro domin su nuna tuba daga aikin ta'addanci da suka saba yi.
Boko Haram: Jawabin rundunar soji
A cewar kakakin rundunar, mika wuyan ya nuna kokarin da rundunar hadin kai a kan yaki da ta'addanci take yi a kan samar da zaman lafiya yana haifar da da mai ido.
Kuma hakan kamar kira ne ga sauran 'yan ta'addan da suke yankin a kan su fito su mika wuya ga jami'an tsaro domin samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
An kashe 'yan Boko Haram a Borno
A wani rahoton kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasarar yin galaba kan ƴan ta'adda a dajin Sambisa da ke jihar Borno ta yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
A wani farmaki da sojojin suka kai cikin dajin sun sheƙe ƴan ta'adda uku tare da lalata maɓoyarsu da suke amfani wajen ɓoyewa
Asali: Legit.ng